EFCC: Dubun wasu manyan Mazambata ta cika a dakin otel

EFCC: Dubun wasu manyan Mazambata ta cika a dakin otel

Jami’an hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa sun damke wasu da ake zargi da laifin zamba ta kafafen yanar gizo a Najeriya kamar yadda mu ka samu labari.

Dakarun na EFCC sun kama wadannan Matasa har su 15 ne a lokacin da su ka kai wani samame a otel dinnan na Blue Chip Hotels da ke cikin Unguwar Rumuigbo da ke Garin Fatakwal a cikin jihar Ribas a cikin makon nan.

Kamar yadda labarin ya zo mana a Ranar Alhamis, 9 ga Watan Mayun 2019, wadannan mutane da aka kama Matasa ne masu shekaru 18 zuwa 30 a Najeriya. Wannan yana cikin kokarin hukumar na yakar Mazambata a Najeriya.

KU KARANTA: Kotu tayi watsi da karar tsohon CJN Walter Onnoghen

EFCC: Dubun wasu manyan Mazambata ta cika a dakin otel

Ibrahim Magu yana kokarin maganin masu zamba cikin aminci
Source: Depositphotos

EFCC sun tabbatar da cewa sun kama Matasan ne bayan sun gano sawun su inda su ka dura masu a daidai lokacin da su ke shakatawa a wannan babban otel dauke da kayan aikin su na manyan wayoyin zamani da kuma gafaka.

Sunayen wadanda aka kama su ne: Tamunotonye Tolofari; Isaac Michael; Kingdom Ekekwu; Daniel Uwalaka; Godswill Agwu; Innocent Daniel; Prince Amaya; Tiemo Ipite; Nduah Gentle; Stella Gbarakoro; da Christiana Cletus.

Sauran wadanda su ka shiga hannun hukumar su ne: Anita Jane; Best Noble, Nduah Precious da kuma Emeka Chibuike Emeka. Daga cikin su akwai Maza 10 da kuma Mata 5 wanda za a maka a gaban kotu ba da dadewa ba inji EFCC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel