Yanzu Yanzu: Kotu ta hana Ganduje aiwatar da sabbin masarautu a Kano

Yanzu Yanzu: Kotu ta hana Ganduje aiwatar da sabbin masarautu a Kano

Babbar kotun jihar Kano ta amince da wani umurni da ke dakatar da Gwamna Abdullahi Ganduje daga aiwatar da rabe-raben masarautar Kano.

Mista Ganduje ya sanya hannu a wata doka a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu wacce ta samar da Karin masarautu hudu, yunkurin da ake yiwa kallo a matsayin kokarin rage darajar Sarki Sanusi Lamido.

A take lamarin ya sauki wani sabon salon siyasa inda mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party a majalisar dokoki suka bayyana cewa ba a samar da karin masarautun guda hudu yadda ya kamata ba, inda suka zargi majalisar da mafi rinjayenta yan All Progressives Congress da rashin bin ka’idojin majalisar.

Yanzu Yanzu: Kotu ta hana Ganduje aiwatar da sabbin masarautu a Kano

Yanzu Yanzu: Kotu ta hana Ganduje aiwatar da sabbin masarautu a Kano
Source: Depositphotos

Mambobin PDP biyu a majalisar dokokin, ciki harda Shugaban marasa rinjaye, sun bayyana wa majiyarmu ta Premium Times cewa sun samu wani umurni daga kotu da ke adawa da samar da sabbin masarautun a maraicen ranar Juma’a, 10 ga watan Mayu.

Yan majalisar sunce ba a yi zaman majalisar yadda ya kamata ba kafin aka yi gaggawan gabatar da dokar a ranar Laraba.

KU KARANTA KUMA: Ganduje ya garzaya Abuja bayan yarimomin Kano 3 sun ki karban tayin zama sarkin Bichi

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Wanban Kano, Aminu Bayero ya amince da nadin da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi masa a matsayin sabon Sarkin Bichi wadda gwamnan ya saka hannu a kan kudirin kafa masarautar a ranar 8 ga watan Mayu.

Daily Trust ta ruwaito cewa an yiwa Aminu, tsohon Sarkin Kano, Marigai Ado Bayero tayin sarautan ne a daren ranar Alhamis amma ya ce yana bukatar lokaci domin ya yi shawara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku latsa domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel