An cafke wani ya yi sata a kamfanin Dangote

An cafke wani ya yi sata a kamfanin Dangote

An gurfanar da wani mutum mai shekaru 41, Taofeek Omotosho a gaban kotun Majisatare da ke zamanta a Ebuta Legas a ranar Juma'a bisa zarginsa da sace na'urorin sanyaya daki (AC) guda 952 da kudinsu ya kai Naira miliyan 7.1.

Sai dai a lokacin da ya bayyana gaban alkali, Omotosho ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da shi.

Mai shigar da karar, Mr Cyril Ejiofor ya shaidawa kotu cewa wanda ake karar ya aikata laifin ne tsakanin Yunin 2018 zuwa Maris din 2019 a Matatar Man Fetur na Dangote da ke Ibeju-Lekki kusa da jihar Legas.

An cafke wani ya yi sata a kamfanin Dangote

An cafke wani ya yi sata a kamfanin Dangote
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnonin APC sun karrama Buhari da lambar yabo (Hoto)

Ya yi ikirarin cewa Omotosho ya sace na'urorin sanyaya daki guda 952 mallakar kamfanin Dangote da kudinsu ya kai Naira miliyan 7.1.

Ejiofor ya ce laifin ya ci karo da sashi na 287 na dokar masu laifi na jihar Legas.

Alkalin kotun, Mr O.O. Olatunji ya bayar da belin Omotosho a kan kudi Naira miliyan daya tare da gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa karban belin.

Ya ce dole daya daga cikin wadanda za su karbi belin Omotosho ya kasance mutum ne mai sana'a.

Daga karshe ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

KU LATSA: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel