Rikicin Majalisa: Manyan APC su na dawowa daga rakiyar matakin Jam’iyya

Rikicin Majalisa: Manyan APC su na dawowa daga rakiyar matakin Jam’iyya

A daidai lokacin da ake shirin kafa Majalisa ta 9 a Najeriya, wasu manyan ‘yan siyasan kasar sun fara lissafin yadda za su yi wajen ganin na-hannun-daman su, sun samu kaso masu tsoka a majalisar.

Wasu daga cikin ‘yan siyasan Arewa su na kokarin ganin sun hana Yaran babban jigon APC watau Bola Tinubu, hana samun kujerun shugabanci a majalisar tarayya. Yanzu haka Bola Tinubu yana tare da Ahmad Lawan da Femi Gbajabimila.

Sai dai yanzu an fara samun wasu daga cikin manyan jam’iyyar APC da su ke kokarin janye goyon bayan da su a ba Sanata Ahmad Lawan da kuma Femi Gbajabimila a zaben majalisa, a sabon yunkurin da ake yi na kassara Bola Tinubu.

KU KARANTA: Ana rikici tsakanin Shugaban Gwamnonin APC da Oshiomhole

Wadannan manyan ‘yan siyasa sun fara hangen cewa Bola Tinubu yana harin kujerar shugaban kasa a 2023, don haka su ke ganin idan aka marawa ‘Yan takarar da yake so baya, zai kara karfi a majalisar tarayya da kuma cikin gidan APC.

Wannan tuburewa da wasu a APC ke yi ne ya jawo takarar Sanata Ali Ndume ta kara karfi a majalisar dattawa kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Vanguard. A wani bangaren kuma ana nakasa takarar Hon. Femi Gbajabimila.

Ko da ba a kira suna ba, a majalisar wakilan tarayya, an fara shirin marawa wasu daga cikin ‘yan majalisar da su ka fito daga Yankin Arewa ta tsakiya, da su tsaya takarar kakakin majalisar wakila a madadin Gbajabimila da APC ta ke so.

KU KARANTA: Maganganun wani Gwamna su neman haddasa fada da Jigon APC

Daga cikin wadanda ake tunani za su kawowa zabin APC cikas a takarar majalisa da za ayi a Watan Yuni sun hada da Honarabul Mohammed Bago da John Dyegh. A halin yanzu akwai masu marawa wadannan ‘yan majalisa baya a cikin manyan APC.

An fara yin wannan kira na taka Bola Tinubu ne bayan da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yayi wani jawabi a jihar Legas inda ya bada shawarar yadda za ayi maganin siyasar Uban-gida a Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel