Kotun zaben shugaban kasa ta gargadi ’yan jarida kan su daina gaggawan yin sharhi

Kotun zaben shugaban kasa ta gargadi ’yan jarida kan su daina gaggawan yin sharhi

Shugabar kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban kasa, Zainab Bulkachuwa tayi barazanar daukar mataki akan lauyoyi, masu kai korafe-korafe da ’yan jarida da aka kama suna sharhi akan duk wata karar da ke a gaban kotun.

Bulkachuwa ta ce duk lauyan da aka kama ya na sharhin kararrakin a kafafen yada labarai bayan zaman kotu, to kotun daukaka kara za ta dauki mataki a kansa.

Ta yi wannan jan kunne ne a yayinda ta ke kaddamar da fara zaman kotun a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu a Abuja.

Ta ce irin wadannan rubuce-rubucen da sharhin na kawo wa kotu cikas da kuma tarnaki ga yanke hukunci. Kuma ya na jefa kokwanto ga jama’a a kan hukuncin da kotu za ta yanke.

Kotun zaben shugaban kasa ta gargadi ’yan jarida kan su daina gaggawan yin sharhi

Kotun zaben shugaban kasa ta gargadi ’yan jarida kan su daina gaggawan yin sharhi
Source: UGC

A karshe ta ce wannan gargadi bai tsallake kan jam’iyyun siyasa da magoya bayan su ba.

KU KARANTA KUMA: Ganduje ya garzaya Abuja bayan yarimomin Kano 3 sun ki karban tayin zama sarkin Bichi

A bangare guda, Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu, ta bayyana cewa Justis Zainab Bulkachuwa, shugabar kotun da ke sauraron karar da Atiku Abubakar ya shigar, mata ce ga Adamu Mohammed Bulkachuwa, wani zababben sanata a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A tsoron cewa Justis Bulkachuwa za ta yi son kai a hukuncinta, jam’iyyar PDP a wata wasika ta nemi ta sauka daga matsayinta a kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel