Gwamnonin APC sun karrama Buhari da lambar yabo (Hoto)

Gwamnonin APC sun karrama Buhari da lambar yabo (Hoto)

- An karrama shugaba Muhammadu Buhari da lambar yabo saboda kwarewarsa wurin jagoranci

- Kungiyar gwamnonin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ce ta bawa shugaba Muhammadu Buhari lambar yabon

- A cewar hadimar shugaba kasa a fanin kafafen sada zumunta, Lauretta Onuchie, an karrama shugaba Buhari ne saboda kokarin da ya yi wurin karbo kudaden Paris Club

Hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin kafafen sada zumunta, Lauretta Onuchie ta bayyana cewa an karrama shugaban kasar da lambar yabo ta musamman saboda kwarewarsa wurin jagorancin al'umma.

Onuchie ta bayyana hakan ne a shafin ta na Twitter a ranar Juma'a 10 ga watan Mayun 2019.

Gwamnonin APC sun karrama Buhari da lambar yabo (Hoto)
Gwamnonin APC sun karrama Buhari da lambar yabo (Hoto)
Source: UGC

Ta ce kungiyar gwamnonin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ce ta bawa shugaban kasar lambar yabon bisa jajircewa da ya yi wurin karbo kudaden Najeriya na Paris Club wadda daga bisani aka rabawa gwamnonin jihohi domin su biya albashi da inganta jihohinsu.

DUBA WANNAN: Su daure mu idan mun yi sata - Gwamnan APC mai barin gado

Onuchie ta kara da cewa lambar yabon godiya ce da gwamnonin suka yiwa shugaban kasar saboda karbo kudin na Paris Club.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartarwa na FEC mafi tsawo tun hawarsa mulki.

Rahotanni sun nuna cewa na fara taron ne misalin karfe 11 na safiya a fadar shugaban kasa kuma ba a kammala taron ba har zuwa karfe 9.30 na dare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel