Wani Lauya ya tafka Buhari kotu kan rashin sanar da majalisar Dokoki da zai tafi Ingila

Wani Lauya ya tafka Buhari kotu kan rashin sanar da majalisar Dokoki da zai tafi Ingila

Inibehe Effiong, wani lauya mai kare hakkin dan adam, mazaunin Legas, ya tafka shugaban kasa Muhammadu Buhari kotu kan tafiya ta kashin kan shi da yayi kwanan nan zuwa kasar Ingila.

A cikin karar mai lamba FHC/L/CS/763/2019 da aka shigar a babbar kotun tarayya dake Legas ranar Alhamis, shugaba Buhari da Abubakar Malami, babban lauyan gwamnatin tarayya sune aka bayyana mutanen da ake kara na daya da na biyu.

Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya sanar ranar 25 ga watan Afirilu cewa “shugaban kasa zai bar Najeriya don wata ziyarar kashin kan shi”.

A cikin kofin na sammacin wanda aka ba kafar watsa labarai ta TheCable, Effiong ya nemi shugaban kasa da ya bayyana ko a cikin tanadin kundin tsarin kasa Kashi na 145 (1) yana da ikon zuwa hutu na tsawon wani lokaci ba tare da aika takardar sanarwa ga shugaban majalisar dattijai da kakakin majalisar wakilai ba.

“Ko wanda ake kara na farko bisa rashin bin ka’idar da kundin tsarin mulkin kasa ya tanada a Kashi na 145 (1) bai saba ma rantsuwar da yayi ba ta kama aiki.“

“Ko tsarin kundin mulkin Njeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara) ko wata doka ta ba wanda ake kara na farko ya gudanar da aikin shugabancin kasa daga wata kasa ta daban ba wai a lokacin da yake akan ziyarar aikin gwamnati zuwa wata kasa ba.”

KU KARANTA: Ambaliyar 2018: Hukumar bada agajin gaugawa ta kasa (NEMA) za ta taimaki manoma 13,965 a jihar Neja

Lauyan yana neman bayani kan cewa ziyarar da Buhari ya kai Ingila cin zarafin doka ne saboda bai aika da takarda zuwa majalisar dokoki ba kafin ya tafi hutun.

Yana kuma bukatar kotu da ta dakatar da Buhari zuwa hutu cikin Najeriya ko kasar waje ba tare da ya aika ma majalisa da takarda ba.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa yace ba dole ba ne shugaban kasa ya sanar da majalisa game da tafiyar kashin kan shi.

“Shugaban kasa bai aikata laifi ba don ya ki aika takarda zuwa ga majalisa kafin ya yi tafiya.”

Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel