Yanzu Yanzu: Kotu ta soke karar da Onnoghen ya daukaka kan hukuncin CCT

Yanzu Yanzu: Kotu ta soke karar da Onnoghen ya daukaka kan hukuncin CCT

Wata kotun daukaka kara a Abuja a ranar Juma’a, 10 ga watan Mayu ta soke wani kara da tsohon Shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen ya daukaka, akan hukuncin da kotun kula da da’ar ma’aikata ta yanke akan kaddamar da kadarorinsa.

A karar da ya daukaka Onnoghen ya kalubalanci umurnin da kotun CCT ta bayar a ranar 23 ga watan Janairun 2019, akan dakatar dashi daga matsayinsa har zuwa lokacin da za a gama shari’arsa da ke gaban kotun.

Kotun daukaka karar a hukuncinta ta bayyana cewa kotun CCT ta kammala abubuwan da ya kamata akan lamarin kaddamar da kadarorin Onnoghen, wanda ya zo karshe a amincewa da tsohon CJN din yayi akan tuhumar kin kaddamar da ainahin kadarorinsa.

Yanzu Yanzu: Kotu ta soke karar da Onnoghen ya daukaka kan hukuncin CCT
Yanzu Yanzu: Kotu ta soke karar da Onnoghen ya daukaka kan hukuncin CCT
Source: Original

KU KARANTA KUMA: Sheikh Daurawa, Abba Koki da Kandahar sun yi murabus daga gwamnatin Ganduje

Kotun daukaka karar a hukuncinta wanda Justis Stephen Adah ta jagoranta, tace umurnin kotun CCT na bangare daya ya take hakkin tsohon Shugaban alkalin wajen rashin ba da damar jin ta bakin shi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa An kammala shiri tsaf domin kotun daukaka kara ta zartar da hukunci game da karan da Shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen ya shigar a gabanta.

Kotun daukaka karan za ta zartar da hukunci a ranar Juma’a, 10 ga watan Mayu, kamar yadda yake kunshe a gajeren jawabin da Sa’adatu Musa Kachalla, kakakin kotun ta saki a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Buga wannan wasan domin samun karin falala a wannan wata na Ramada: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel