Dalilin da yasa na yafe ma wanda yayiwa diyata fyade

Dalilin da yasa na yafe ma wanda yayiwa diyata fyade

-Wani mutum mai suna Abdullahi Bala yayiwa yarinya yar shekara 9 fyade

-Mahaifin yarinyar yace ya bar wannan mutum da Allah saboda bai son tashin hankali

Ibrahim Muhammad mahaifin wata yarinya yar shekara 9 da haihuwa wacce akayiwa fyade, ya bayyana dalilinsa na gafartawa mutumin da ya aikata hakan ga diyarsa.

Wanda ake zargin mai suna, Abdullahi Bala shekaru 33 da haihuwa ya karyata zargin da ake yi masa. Ana zarginsa da aikata wannan laifin ne a shiyyar Aduwawa kwatas dake karamar hukumar Ikpoba-Okha a jihar Edo ranar 8 da 9 ga watan Fabrairu, 2019 inda ya fake da koyawa yarinyar karatu.

Dalilin da yasa na yafe ma wanda yayiwa diyata fyade

Dalilin da yasa na yafe ma wanda yayiwa diyata fyade
Source: UGC

KU KARANTA:Hukumar yan sanda zata sanya na’urar daukan hoto a wasu muhimman wurare, inji IGP

Yarinyar ta shaidawa kotun lamuran iyali ta Edo cewa sau biyu anayi mata fyade. Ibrahim yace ya barwa Allah hukunci saboda shi mutum ne mai kaunar zaman lafiya.

Mahaifin yace zai yi iya bakin kokarinsa ganin cewa diyarsa ta samu ilimi mai inganci kamar yadda sauran yara ke samu.

Shugaban kotun D.I Adamaigbo da yake bayani akan lamarin, ya gargadi wanda ak zargi da laifin kan ya bar yin karyar cewa bai aikatawa yarinyar fyade ba.

A karshe kuma ya gargadi Abdullahi da ya tuba ya bar aikata irin wannan dayen aiki.

A wani labari mai kamar wannan, shugaban hukumar yan sanda Adamu Mohammed yace zasu sanya na'urar CCTV a wasu daidaikun wurare domin inganta sha'anin tsaro Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA: Domin karuwa cikin wannan watan mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel