Sarki a karkashin shugaban karamar hukuma ya ke - Ganduje

Sarki a karkashin shugaban karamar hukuma ya ke - Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yana karkashin shugaban karamar hukuma ne ba gwamnan jiha ba.

Ganduje ya yi wannan furuci ne yayin da ya ke martani a kan kuce-kuce da ya kunno kai sakamakon sanya hannu kan dokar kirkirar sabbin masarautu hudu a Kano da wasu ke cewa bita da kulli ake yiwa Sanusi.

Sarki a karkashin shugaban karamar hukuma ya ke - Ganduje

Sarki a karkashin shugaban karamar hukuma ya ke - Ganduje
Source: Facebook

"Muna son mu kai Kano mataki ne gaba ne kuma muna bukatar gudunmawa daga sarakunan gargajiya musamman a fannin ilimi, tsaro da noma.

"Kirkirin sabbin masarautun da mu kayi ya samo asali ne a tarihi. Shekarun baya ba haka lamarin ya ke ba," inji Ganduje.

DUBA WANNAN: Kirkirar sabbin masarautu: Mutanen Kano ba za su lamunta ba - Naniya

"Wannan ba bita da kulli bane, babu wata matsala tsakani na da shi, hasali ma kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ta ce Sarki yana karkashin shugaban karamar hukuma ne.

"Idan yana da matsala sai ya tuntubi shugaban karamar hukuma ya tattauna da shi ba gwamna ba. Al'ummar Kano sunyi murnar wannan matakin na krkiran sabbin masarautun kuma zamu tabbatar sun kawo cigaba a jihar Kano," Ganduje ya fadawa manema labarai na gidan gwamnati a Abuja.

A ranar Laraba ne Ganduje ya rattaba hannu a kan kudirin doka na kirkirar sabbin masarautu hudu; Gaya, Rano, Karaye da Bichi wadanda za su kasance a karkashin masarautar Kano.

Ku biyo mu domin karin bayani ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel