Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) za ta yi zanga-zangar kin jinin Ngige, tayi kira ga ma’aikata su kunyata shi

Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) za ta yi zanga-zangar kin jinin Ngige, tayi kira ga ma’aikata su kunyata shi

- NLC ta zargi Ngige da daukar nauyin wani harin da aka kai ma masu zanga-zangar da suka je gidansa na Abuja

- Ngige ba ya da damar canja mukamin da shugaban kasa yayi

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta umurci mambobinta da su kunyata ministan kwadago da ayukka, Chris Ngige da iyalansa.

Kungiyar ta kwadago ta sanar cewa za a gudanar da wata zanga-zangar matakin kasa a Abuja, ranar Litinin don nuna rashin jin dadi kan amfani da ‘yan ta’adda kan mambobinta, wadanda suka gudanar da zanga-zangar lumana.

NLC ta zargi Ngige da daukar nauyin wani harin da aka kai ma masu zanga-zangar da suka je gidansa na Abuja

Sunyi zanzangar ne saboda zargin da aka yi na cire wani mamba, ma’aikacin Asusun Inshura na kasa (NSITF) daga hukumar gudanarwa.

Da farko ministan yaki kaddamar da hukumar ta NSITF saboda zargin da ake na wata almundahana.

A lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi bayan kammala wani taro ranar Alhamis, shugaban kungiyar kwadago na kasa Ayuba Wabba, yace Ngige ba ya da damar canja mukamin da shugaban kasa yayi kan cewa bai taba bada sunan Frank Kokori ya jagoranci hukumar gudanar da NSITF ba.

KU KARANTA: Ambaliyar 2018: Hukumar bada agajin gaugawa ta kasa (NEMA) za ta taimaki manoma 13,965 a jihar Neja

“Bai cancanci ya zama minista ba. Ba ya da wani dalilin da zai sa a kira shi minitan kwadago, shi son kansa yake, kuma maimakon bada kariya gare mu yana takura muna ne. Don haka ba muda wani abunyi da shi.”

“NLC ta aika da sako zuwa ga kasashe 163 wadanda suke mambobi ne na ITUC, su kunyata ministan da iyalansa a duk inda aka gan su, musamman a filayen jiragen sama inda ma’aikata ke aiki.”

“Dalilin da ya sa yake adawa da Cif Kokori shine tsohon ma’aikacin ba ya bada kai bori ya hau. Tunda yake ministan na maganar almundahana a NSITF ne, to kamata yayi gwamnati ta kafa wani kwamitin bincike don gano hakikanin masu almundahanar."

“Muna bukatar a kaddamar da hukumar gudanarwar dake karkashin Kokori, kuma ‘yan ta’addar da suka ci zarahinmu a gaban jami’an tsaro a bincike su, a gurfanar da su a gaban kuliya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel