Dalilin da yasa na kafa sabbin masarautu a Kano – Ganduje

Dalilin da yasa na kafa sabbin masarautu a Kano – Ganduje

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano yace ya yanke shawarar samar da sabbin masarautu hudu ne a jihar saboda ya kai jihar zuwa mataki na gaba.

A ranar Laraba, 8 ga watan Mayu ne majalisar dokokin jihar ta gabatar da wata doka na kacaccala masarautar Kano zuwa gida biyar.

Kuma Ganduje ya sanya hannu sannan ya aiwatar da dokar a wannan ranar.

Mutane da daman a ganin Ganduje ya samar da sabbin masarautun don ya rage iko da mulkin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, kan banbancin siyasa.

Dalilin da yasa na kafa sabbin masarautu a Kano – Ganduje

Dalilin da yasa na kafa sabbin masarautu a Kano – Ganduje
Source: Twitter

Sai dai, da yake jawabi ga manema labarai a fadar Shugaban kasa, Ganduje yace mutanen da ke Allah wadai da hukuncin “na da damar nuna ra’ayinsu amma za mu kai Kano zuwa mataki na gaba ne sannan muna bukatar tsarin al’ada tsayayye wanda za a dama dasu, musamman a bangarorin ilimi, tsaro da noma.”

Yayi bayanin ne a gefe guda na taron karammawa na kungiyar gwamnoni da ke gudana a fadar Shugaban kasa, Abuja.

Yace an rarraba masarautar ne saboda jihar Kano ‘na bukatar jjircewar sarakunan gargajiya.

"Ta hanyar raba tsarin, muna bin tarihi ne. Shekarun baya tunma kafin shekaru 800 da kuke magana a kai, lamarin ba haka yake ba.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Daurawa, Abba Koki da Kandahar sun yi murabus daga gwamnatin Ganduje

"Don haka idan an kafa abu shekaru 800 da suka gabata, abubuwa na ci gaba yanzu kuma za a samu wasu shekaru 800 anan gaba. Don haka ku duba tarihin.

"Don haka, ba muzgunawa bane, bana adawa dashi. Duba, kamata yayi ma ya dunga tattaunawa da shugaban karamar huku, bisa ga kundin tsarin kasar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel