Wasu abubuwa da Atiku zai yi idan bai samu nasara a kotu ba

Wasu abubuwa da Atiku zai yi idan bai samu nasara a kotu ba

- Showunmi ya bayyana cewa Atiku ya yi alkawarin ba zai bari 'yan Najeriya su fuskanci wani rikici ko tashin hankali ba saboda nashin nasarar shi a zabe

- Sannan ya kara da cewa koda yake Atiku na da tabbacin cewa zai yi nasara a kotu, saboda haka Atiku ne shugaban kasa a zuciyar 'yan Najeriya

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa, PDP ya ce zai yi karbi hukuncin da kotu ta yanke game da karar da ya shigar akan magudin zabe, in ji wani na hannun daman sa, Segun Showunmi.

Ya kara da cewa, duk da haka, akwai alamun cewa Atiku zai samu nasara a kotun.

Karar da dan takarar ya kai ta kalubalanci sanarwar da hukumar zabe ta kasa ta bayar da ke nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya lashe zabe.

Showunmi ya ce Atiku ya yi alkawarin ba zai bari 'yan Najeriya su fuskanci wani rikici ko tashin hankali saboda faduwar shi zabe ba.

Wasu abubuwa da Atiku zai yi idan bai samu nasara a kotu ba
Wasu abubuwa da Atiku zai yi idan bai samu nasara a kotu ba
Source: UGC

Tsohon mataimakin shugaban kasar, a cewar Showunmi, ya mai da hankali wurin ganin an samu gyare-gyare wanda zai inganta cigaban kasa baki daya.

Majiyarmu LEGIT.NG ta nuna cewa, Showunmi wanda ya yi magana da manema labarai a Abuja, ya nuna cewa akwai alamun nasara a karar da suka shigar kotu.

Ya karyata jita-jitar da ake yadawa da ke nuni da cewa Atiku ya nemi taimakon kasashen waje.

KU KARANTA: Sojoji sun yi nasarar cafke masu kerawa 'yan ta'adda makamai

Ya ce duk yadda mutane zasu kalli zaben, kowa ya san Atiku ne ya lashe zaben shugaban kasar.

Hakazalika majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton cewa Peter Obi, wanda ya fito a matsayin mataimaki ga Atiku Abubakar, ya halarci zaman kotun da aka gabatar ranar Laraba 8 ga watan Mayu, 2019.

Bayan haka kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci kotun da ta ke sauraron karar zaben da ta yi watsi da karar da Atikun ya shigar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel