Hukumar yan sanda zata sanya na’urar daukan hoto a wasu muhimman wurare, inji IGP

Hukumar yan sanda zata sanya na’urar daukan hoto a wasu muhimman wurare, inji IGP

-Shugaban hukumar yan sanda ya nemi jami'an yan sanda dasu kara jajircewa wurin ganin bayan ta'addacin dake addabar Najeriya

-Mohammed Adamu ya sake cewa, dole jami'i ya kula da doka yayin gudanar da aikinsa saboda sabawa dokar kan yi sanadiyar korarsa daga aiki.

Mukaddashin sufeton yan sanda Mohammed Adamu a jiya yayi kira ga sashen rundunar yan sanda dake yaki da yan fashi wato SARS da sauran sassa na musamman karkashin rundunar yan sanda dasu zage dantse domin fada da ta’addanci.

Ya sake cewa duk jami’in da aka same shi da hannu wurin ketare iyaka yayi gudanar da aiki ko kuma kisa nab a gaira ba dalili, zai fuskanci horo mai tsanani wanda kan iya sanadiyar korarsa daga aiki.

Hukumar yan sanda zata sanya na’urar daukan hoto a wasu muhimman wurare, inji IGP

Hukumar yan sanda zata sanya na’urar daukan hoto a wasu muhimman wurare, inji IGP
Source: UGC

KU KARANTA:Abin mamaki: Uwa ta sayar da diyarta kan kudi kalilan

Shugaban hukumar yan sandan yace, hukamarsa nada niyyar sanya na’urar daukan hoto wacce akafi sani da CCTV a wasu muhimman wurare domin taimakawa wurin yaki da ta’addanci.

Adamu yayi wannan jawabin ne wurin wata ganawa da yayi da jami’an yan sandan SARS, sashen dake fada da masu garkuwa da mutane da wasu sassa na musamman dake karkashin hukamar ta yan sanda a shelkwatarsu dake Abuja.

“ I na shawartarku da ku kara kaimi yayin gudanar da ayyukan ku, har ila yau yaki da ta’addanci sam baiyi kama da sabawa doka ba. Dole sai kun bi doka yadda ya dace yayin gudanar da aikin naku.

“ Bari na gargade ku kamar yadda na saba yi, duk jami’in da aka samu da hannu wurin aikata kisa ba kan ka’ida ba ko kuma ya sabawa dokar aikinmu, tabbas zai fuskanci matsanancin hukunci. Ba a nan kawai hukunci ya tsaya ba, zai ma iya rasa aikinsa daga bisani kuma ya gurfana gaban shari’a.

“ Ku a matsayinku na masu lura da abinda kananan jami’ai keyi, idan har kuka gaza yin abinda ya dace zaku fuskanci hukunci.” A cewarsa.

Adamu ya sake cewa, kari akan baku kwarin guiwar gudanar da aiki: “ Zamu sake habbaka sha’anin tsaro akan manyan tituna da taken ‘Safer Highway Patrol’. Wannan zai kasance domin tabbatar da tsaro mai inganci akan hanyoyinmu musamman wadanda matafiya ke kaiwa da komowa.” A fadar Adamu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel