Ambaliyar 2018: Hukumar bada agajin gaugawa ta kasa (NEMA) za ta taimaki manoma 13,965 a jihar Neja

Ambaliyar 2018: Hukumar bada agajin gaugawa ta kasa (NEMA) za ta taimaki manoma 13,965 a jihar Neja

- An tantance manoman ta hanyar kidayar da aka yi cikin kananan hukumomin mulki 16, wadanda suka hadu daiftila’in ambaliyar a shekar 2018.

- Hukumar bada agajin ta kasa za ta hada kai da takwararta ta jihar Neja (NSEMA), da ma’aikatar aikin gona da hukumar bunkasa aikin gona ta jiha (NAMDA) don tantance manoman gaskiya.

Hukumar bada agajin gaugawa ta kasa (NEMA) a jihar Neja, za ta taimaka ma manoma 13,965 da kayan aikin gona, wadanda aka tababatar sunyi hasarar amfanin gonarsu a lokacin ambaliyar ruwan da ta faru cikin shekarar 2018, kamar yadda mai kula da ofishin hukumar dake Minna Mrs Lydia Wagami ta sanar.

Wagami tace an tantance manoman ta hanyar kidayar da aka yi cikin kananan hukumomin mulki 16, wadanda suka hadu daiftila’in ambaliyar a shekar 2018.

“Kananan hukumomin mulkin da abun ya shafa sun hada da Bosso, Shiroro, Borgu, Agwara, Mokwa, Edati, Lavun, Lapai, Agaie, Katcha, Kontagora, Paiko, Wushishi, Gurara, Gbako da Rafi. Kowane daga cikin manoman za ba shi agajin noma dai-dai girman hasarar da yayi.”

Wagami tace hukumar bada agajin ta kasa za ta hada kai da takwararta ta jihar Neja (NSEMA), da ma’aikatar aikin gona da hukumar bunkasa aikin gona ta jiha (NAMDA) don tantance manoman gaskiya.

KU KARANTA: 'Yan PDP ku hada kai da Buhari don ci gaban kasa - In ji Emmanuel Umohinyang

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumar bada agajin gaugawa ta kasa (NEMA) da su kirga manoma a cikin jihohi 18 da ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2018 a taimaka ma su, don inganta noma da tabbatar da samun isasshen abinci a kasar nan.

Alhaji Haruna Dukku, Kwamishinan aikin gona na jihar ya yaba ma gwamnatin tarayya kan kokarinta na taimakon manoma a jihar, tare da kira ga manoman dasu bada hadin kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel