Oshiomhole na farauta ta, bayan ni na sa ya zama shugaban jam'iyya - Rochas Okorocha ya koka

Oshiomhole na farauta ta, bayan ni na sa ya zama shugaban jam'iyya - Rochas Okorocha ya koka

- Gwamnan jihaar Imo mai barin gado Rochas Okorocha ya bayyana cewa shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole ne ya ke yi masa zagon kasa a harkar siyasa

- Ya bayyana cewa shine wanda ya tsaya tsayin daka wurin ganin ya zama shugaban jam'iyyar amma sai gashi yanzu shine yake farautar shi

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya zargi shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, da farautarsa bayan ya gama wahalar dora shi akan kujerar shugaban majalisar.

"Babu wani abu da ke tsakanina da Adams Oshiomhole, illa kawai na san ya daya daga cikin mutanen da suke hada mini makirci don kawo karshena a siyasa," a cewar Okorocha a wani taron manema labarai a Abuja.

"Abin bakin ciki shi ne Adam Oshiomhole wanda na yi wahalar dora shi akan kujerar shugaban jam'iyya shi ne yanzu ya ke son ganin karshena."

Oshiomhole na farauta ta, bayan ni na sa ya zama shugaban jam'iyya - Rochas Okorocha ya koka

Oshiomhole na farauta ta, bayan ni na sa ya zama shugaban jam'iyya - Rochas Okorocha ya koka
Source: Twitter

Okorocha ya faraa samun matsala da shugabannin jam'iyyar APC ne tun lokacin da aka gabatar da babban zabe a kasar nan inda dan takararsa Uche Nwosu ya sha kasa a hannun Sanata Hope Uzodinam.

Cikin rashin jin dadin abinda ya faru Okorocha ya ta ya Nwosu yakin neman zabe wanda ya koma jam'iyyar Action Alliance (AA) don fitowa takarar gwamna amma ita ma ya sha kasa.

A daya bangaren kuma, Okorocha ya lashe zaben Sanatan jihar Imo ta yamma, a zaben da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA: Wani mutumi ya datsewa matarsa yatsu saboda ta fara karatun digiri

Amma hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, ta ki amincewa da samun nasarar ta sa.

Hakazalika, Okorocha ya bayyana cewa hana shi takardar lashe zabe da hukumar zabe ta yi, na da alaka da wasu manya na jam'iyyar APC da suke son ganin bayansa a siyasance.

"Ban taba tambayar Oshiomhole wani abu ba, abinda na nema shine kawai ya yi abinda ya kamata," in ji Okorocha.

Okorocha, wanda ya ke tsohon dan jam'iyyar adawa ta PDP, ya ce irin wannan halin da ya ke ciki a yanzu ne ya sanya shi dawowa jam'iyyar APC a shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel