Yanzu Yanzu: An yanto yara 894 daga hannun Boko Haram

Yanzu Yanzu: An yanto yara 894 daga hannun Boko Haram

- Yan aikin sa kai na Civilian JTF sun ‘yanto kusan yara 900 da Boko Haram ke ajje dasu a yankin Arewa maso gabas

- 106 daga cikin yaran guda 894 da aka 'yanto duk mata ne

A yau juma’a, 10 ga watan Mayu ne aka ‘yanto kusan yara 900 da Boko Haram ke ajje dasu a yankin Arewa maso gabas.

Yan aikin sa kai na Civilian JTF da ke taimaka wa sojoji wajen yaki day an ta’addan ne suka ceto yaran guda 894 din, wadanda 106 daga cikinsu mata ne.

Majalisar dinkin duniya ce ta bayyana hakan, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Abin mamaki: Uwa ta sayar da diyarta kan kudi kalilan

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa manoma a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana yadda suke cikin mummunan tashin hankali sanadiyyar sace sacen mutane, sun bayyana cewa 'yan bindiga suna karbar haraji a wurinsu kafin su basu damar shiga gonakinsu.

Sun ce bayan haka, yawancin su an tilasta musu barin gonakin su, inda suka kara cewa matsalar baza ta kau ba har sai an dauki matakan gaggawa akan 'yan bindiga dake addabar yankin nasu; sun kuma kara da cewa muddin ba a dauki mataki ba matsalar karancin abinci za ta kunno kai a fadin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel