Okorocha yana girmama Buhari da APC duk da korafin da ya ke yi - Bagudu

Okorocha yana girmama Buhari da APC duk da korafin da ya ke yi - Bagudu

- Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya yi tsokaci a kan kalaman takwararsa na Imo, Rochas Okorocha

- A ranar Alhamis 9 ga watan Mayu ne Okorocha ya ce sharin da ya hadu da shi a APC ya fi wanda ya ke tsoron haduwa da shi a PDP sau 10

- Gwamna Bagudi ya ce har yanzu Okorocha yana nan a APC saboda yana girmama shugaba Muhammadu Buhari

Okorocha yana girmama Buhari da APC duk da korafin da ya ke yi - Bagudu

Okorocha yana girmama Buhari da APC duk da korafin da ya ke yi - Bagudu
Source: Facebook

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya ce takwararsa na jihar Imo, Rochas Okorocha yana mutunta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) hakan ya sa bai fice daga jam'iyyar ba.

A hirar da akayi da Bagudu a Channels Televisin, ya ce duk da cewa Okorocha baya jin dadin abubuwan da ke faruwa da shi a cikin jam'iyyar a halin yanzu amma yana nan daram dam a jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Su daure mu idan mun yi sata - Gwamnan APC mai barin gado

Ya ce Okorocha yana matukar girmama shugaba Muhammadu Buhari inda ya kare da cewa girmama jam'iyyar ta ya keyi ne yasa bai fice daga jam'iyyar ba.

"Bai ji dadin wasu abubuwa da suka faru da shi ba ko abubuwan da ya ke tsamanin anyi masa kuma ina ganin ya yi takatsantsan wurin banbanta su," inji Bagudu.

Bagudu ya yi wannan tsokacin ne sakamakon ikirarin da Okorocha ya yi na cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar ta APC suna yi masa bita da kulli inda har ya ce sharin da ya hadu da shi a APC ya fi wanda ya ke tsoro a PDP sau 10.

"Abin takaici ne yadda jam'iyyar ta na taimaka wurin kafa ta take wulakanta ni. Sharin da ya hadu da shi a APC ya fi wanda ya ke tsoron hadu da shi a PDP sau 10."

Bagudu ya yi bayanin cewa duk da bacin ran da Okorocha ya yi, shine jagoran gwamnonin jam'iyyar APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel