Samar da sabbin masarautu 4: Al’umman Kano sun yi zanga-zanga

Samar da sabbin masarautu 4: Al’umman Kano sun yi zanga-zanga

- Kungiyar matasa a Kano sun gudanar da zanga-zangan nuna rashin jin dadi akan samar da sabbin masarautu hudu a jihar

- Kakakin kungiyar yace akwai banbanci tsakanin masarauta da sarki, inda ya kara da cewa ba daidai bane daukarsu a matsayi guda

- A cewar kungiyar, akwai lamura da ke bukatar kula fiye da samar da karin masarautu

Al'umman jihar Kano a jiya Alhamis, 9 ga watan Mayu sun yi zanga zanga a birnin Kano bisa kafa sabbin masarautu hudu a jihar.

Masu zanga zanga a karkashin kungiyar Kano First Forum sun bayyana rashin jin dadinsu akan lamarin.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a lokacin zanga zangan, kakakin kungiyar Dr. Yusuf Ishaq Rabiu, yace mutanen jihar sun kasance tare da bukatan ingantacciyar cibiyar kiwon lafiya, makarantu da ingantattun kayan more rayuwa, ba zance karin masarautu ba.

Samar da sabbin masarautu 4: Al’umman Kano sun yi zanga-zanga

Samar da sabbin masarautu 4: Al’umman Kano sun yi zanga-zanga
Source: Depositphotos

“Akwai muhimmanci a fahimci cewa akwai bambanci tsakanin masarauta da kuma sarki. Ba daidai bane a gudanar da ayyukan biyu a lokaci guda.

"Dangane da wannan lamarin, majalisar dokokin jihar Kano bata yi adalci ga mutanen jihar Kano ba kuma jihar ta kasance da muhimman bukata, cewa akwai bukatan mayar da hankali akan fanin ilimi, ruwa, cibiyar kiwon lafiya da rashin cigaban tattalin arzikin jihar."

KU KARANTA KUMA: Ba za ki iya rike shari’an Atiku ba, mijinki sanatan APC ne – PDP ga Justis Bulkachuwa

Ya ce, “Cikin bakin ciki, mu yan kungiyar Kano First Forum, mun gudanar da zanga zangan don nuna rashin jin dadi bisa lamarin da ya auku tsakanin majalisar dokokin jihar da gwamnatin jihar Kano.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel