Kotun daukaka kara za ta yanke hukunci kan Onnoghen a yau

Kotun daukaka kara za ta yanke hukunci kan Onnoghen a yau

- Kotun daukaka karat a kammala shiri tsaf domin yanke hukunci akan shari’an da Shugaban alkalan kasar Onnoghen ya shigar gabanta kan hukuncin CCT

- Kotun daukaka karan ta tabbatar da cewa za ta yanke hukunci a ranar Juma’a, 10 ga watan Mayu

- Daga cikin lamarin da kotun daukaka karan za ta duba shine ko kotun CCT na da iko akan shari’an Onnoghen

An kammala shiri tsaf domin kotun daukaka kara ta zartar da hukunci game da karan da Shugaban alkalan Najeriya, Walter Onnoghen ya shigar a gabanta.

Kotun daukaka karan za ta zartar da hukunci a ranar Juma’a, 10 ga watan Mayu, kamar yadda yake kunshe a gajeren jawabin da Sa’adatu Musa Kachalla, kakakin kotun ta saki a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu.

Kotun daukaka kara za ta yanke hukunci kan Onnoghen a yau

Kotun daukaka kara za ta yanke hukunci kan Onnoghen a yau
Source: Original

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa jawabin ya bayyana a takaice: “An bayar da sanarwa. Karar da Justis Walter Onnoghen ya shigar ya isa yanke hukunci, a safiyar gobe (Juma’a, 10 ga watan Mayu) a reshen Abuja. Mun gode da hadin kanku a koda yaushe.”

KU KARANTA KUMA: Mun kama wasu – Shugaban tsaro ya yi jawabi kan garkuwa da surukin Buhari

A kan lamura 16, Onnoghen ya daukaka hukuncin kotun kula da da’ar ma’aikata (CCT) wacce ta kaddamar dashi a matsayin mai laifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel