Ba za ki iya rike shari’an Atiku ba, mijinki sanatan APC ne – PDP ga Justis Bulkachuwa

Ba za ki iya rike shari’an Atiku ba, mijinki sanatan APC ne – PDP ga Justis Bulkachuwa

- Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sanya zargi akan karar da tsoon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya shigar game da zaben Shugaban kasa

- PDP ta bayyana cewa alkalin da ke rike da shari’an Atiku, Zainab Bulkachuwa, ta kotun daukaka kara ta kasance mata ga zababben sanatan jam’iyyar All Progressives Congress (APC)

- Jam’iyyar adawan ta nemi Zainab ta janye daga matsayinta na Shugabar kotun da ke zama kan lamarin, tare da tsoron cewa tana iya yin son kai a shari’anta

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu, ta bayyana cewa Justis Zainab Bulkachuwa, shugabar kotun da ke sauraron karar da Atiku Abubakar ya shigar, mata ce ga Adamu Mohammed Bulkachuwa, wani zababben sanata a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A tsoron cewa Justis Bulkachuwa za ta yi son kai a hukuncinta, jam’iyyar PDP a wata wasika ta nemi ta sauka daga matsayinta a kotun.

Ba za ki iya rike shari’an Atiku ba, mijinki sanatan APC ne – PDP ga Justis Bulkachuwa

Ba za ki iya rike shari’an Atiku ba, mijinki sanatan APC ne – PDP ga Justis Bulkachuwa
Source: Facebook

Jam’iyyar adawar, a wata wasika dauke das a hannun shugabanta da sakatarenta, Prince Uche Secondus da Sanata Umar Tsauri, ta jadadda cewa babu tabbacin kasancewa a tsakiya a bangaren alkalin.

KU KARANTA KUMA: Mun kama wasu – Shugaban tsaro ya yi jawabi kan garkuwa da surukin Buhari

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Atiku Abubakar dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, zai amince da hukuncin kotun zabe game da karar da ya shigar, hadimins,Segun Showunmi ya bayyana.

Ya kara da cewa, sai dai akwai alamu da ke nuna cewa Atiku zai samu yancinsa.

Karar da yashigar na kalubalantar sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zabe wada hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel