Mun kama wasu – Shugaban tsaro ya yi jawabi kan garkuwa da surukin Buhari

Mun kama wasu – Shugaban tsaro ya yi jawabi kan garkuwa da surukin Buhari

- Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas ya bayyana cewa an kama wasu a kan garkuwa da Alhaji Musa Umar Uba

- Ibas ya ba da tabbacin cewa za a ceto basaraken kuma surukin shugaba Buhari kwanan nan

- Anyi garkuwa da Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba a ranar 1 ga watan Mayu, 2019 a Daura, jihar Katsina

Kwana tara bayan garkuwa da surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, har yau ba a sako shi ba.

Anyi garkuwa da Uba, babban mai bada shawara ga majalisar masarautar Daura a ranar 1 ga watan Mayu, a gidansa.

Daily Trust ta rahoto cewa kwana tara bayan afkuwar lamarin, basaraken wanda ya kasance mijin yar’uwar Buhari, Hajiya Bilkis, na a hannun wadanda suka yi garkuwa dashi.

Mun kama wasu – Shugaban tsaro ya yi jawabi kan garkuwa da surukin Buhari

Mun kama wasu – Shugaban tsaro ya yi jawabi kan garkuwa da surukin Buhari
Source: UGC

A karshen tattaunawa tare da Buhari a fadar shugaban kasa, Abuja a jiya, shuwagabannin tsaro sun ce an kama wasu da ke da hannu cikin lamarin.

Shugaban hafsan sojin ruwa, Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas, wada yayi Magana a madadin takwarorinsa, yace: “ana ci gaba da kokari sosai, an kama manyan wadanda ake zargi da hannu a lamarin sannan kuma akwai tabbacin cewa nan da dan lokaci kadan, za a gurfanar da wadanda ke da alhakin mumunan aikin.”

Ibas yace anyi tattaunawa na sa’o’i hudu don yi wa shugaban kasa jawabi akan lamarin tsaro gaba daya, bayan dawowar sa daga tafiyan hutu a kasar waje.

KU KARANTA KUMA: Atiku zai ci gaba da zama Shugaban kasa a zukatan yan Najeriya koda ya fadi - Showunmi

A halin da ake ciki, mun ji cewa majiya biyu masu kusanci da iyalen sun ce har yanzu basu ji bayanai ba akan kokarin da ake yi don kubutar da shi.

Daya daga cikin majiyin ya bayyana cewa sun ji ne a kafofin yada labarai cewa jami’an tsaro sun kama wassu mutane.

Sauran majiyin kuma yace iyalen Magajin Gari da sauran jama’ansa na cikin wani irin hali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel