Wani mutumi ya datsewa matarsa yatsu saboda ta fara karatun digiri

Wani mutumi ya datsewa matarsa yatsu saboda ta fara karatun digiri

- Tsananin kishi da son zuciya sun sanya wani mutumi datsewa matarsa hannu saboda ta fara karatun digiri ba tare da izinin sa ba

- Yanzu haka dai an yankewa mutumin daurin rai da rai, inda ita kuma matar ta koma gidan iyayenta domin cigaba da jinya, kafin ta koma makaranta

Wani mutumi mai tsananin kishi yana fuskantar daurin rai da rai a gidan yari, bayan ya datsewa matarshi hannu saboda ta fara karatun digiri ba tare da izininsa ba.

Rafiqul Islam, mai shekaru 30, ya rufe idon matarsa Hawa Akhter, mai shekaru 21, sannan ya rufe mata baki, inda yake gaya mata cewa zai ba ta wata kyauta mai ban mamaki.

Maimakon ya bata kyauta sai ya sa ta rike hannunta, inda ya datse 'yan yatsunta duka guda biyar din. Daya daga cikin 'yan uwansa kuma ya jefa yatsun matar a cikin shara don kada likitoci su gani har su samu damar mai da mata.

Wani mutumi ya datsewa matarsa yatsu saboda ta fara karatun digiri

Wani mutumi ya datsewa matarsa yatsu saboda ta fara karatun digiri
Source: Depositphotos

Mista Islam, wanda yake ma'aikacine a hadaddiyar daular Larabawa, ya gargadi matarsa cewa zai yi mata hukunci mai tsanani mutukar bata hakura da karatu ba.

Mohammed Saluddin, babban jami'in 'yan sanda na Bangladesh ya bayyana cewa Mista Islam ya amsa laifin sa bayan an kama shi a birnin Dhaka, kuma zai fuskanci hukunci daurin rai da rai a gidan kurkuku.

KU KARANTA: Dalibin Sakandare ya kashe abokinsa akan budurwa a jihar Katsina

Ms Akther ta ce yanzu haka ta na koyon rubutu ne da hannun hagu, kuma za ta yi kokarin cigaba da karatun ta. Yanzu haka dai ta koma gidan iyayenta da zama.

A watan Yunin shekarar 2018, wani mutumi marar aikin yi ya kwakwale idon matarsa, a birnin Dhaka, saboda ba zai iya zuba mata ido ta na karatu a wata jami'ar kasar Canada ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel