An kashe wani jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas

An kashe wani jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas

- Wani babban jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas ya gamu da ajalinsa bayan da wasu 'yan bindiga suka je har unguwarshi suka harbe shi

- Mutumin wanda ya taba fitowa takarar dan majalisar wakilai ya gamu da ajalinsa a daren jiya da misalin karfe 8:45 na dare

Wasu 'yan bindiga sun harbe jigo na jam'iyyar All Progressive Congress, Omunakwe Benson.

An kashe Omunakwe a unguwar Agip Estate da ke garin Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers, jiya Laraba.

An ce 'yan bindigar sun shiga cikin unguwar suka harbi mutumin, wanda shi ne tsohon dan takarar majalisar dokoki, a yayin da yake dawowa gida da misalin karfe 8:45 na dare.

Wani dan uwa ga marigayin, Okechukwu Benson, ya ce yana kallon wasan kwallon kafa, sai ya samu kiran waya, inda ake bayyana mishi cewa an harbe dan uwanshi.

An kashe wani jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas

An kashe wani jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas
Source: Facebook

"Na samu kiran waya da misalin karfe 9 na dare, inda ake sanar da ni cewa an harbe dan uwana. Ba shi da matsala da kowa, wanda har zai bayar da damar a kashe shi," inji Okechukwu.

Sai dai ya yi kira ga hukumar 'yan sandan jihar da su binciko wadanda ke da hannu a kisan dan uwan nashi.

KU KARANTA: Dalibin Sakandare ya kashe abokinsa akan budurwa a jihar Katsina

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa an kama mutane biyu da ake zargin suna da hannu a kisan.

"Lamarin ya faru jiya da daddare, 'yan bindiga sun kai mishi hari. Amma yanzu mun kama mutane biyu kuma suna taimaka mana wurin binciken mu," in ji Omoni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel