'Yan PDP ku hada kai da Buhari don ci gaban kasa - In ji Emmanuel Umohinyang

'Yan PDP ku hada kai da Buhari don ci gaban kasa - In ji Emmanuel Umohinyang

- "Saboda hankalin ‘yan siyasar na wurin yadda za su shirya kansu a cikin jam’iyyunsu. Amma da yake yanzu zabe ya wuce da ‘yan siyasar da suka ci zabe da wadanda ba su ci ba duk sun samar da makamai ga ‘yan bangarsu, kuma ba su iya karbar makaman daga hannuwansu.”

- Kamata yayi ‘yan jam’iyyar PDP su hada kai da shugaban kasa Muhammadu Buhari don samar da cigaban kasa.

A wata hira da jaridar LEADERSHIP tayi da wani mai fashin bakin al’amurran yau da kullum, Emmanuel Umohinyang, wanda ya taka rawa wurin sake zaben Buhari a karkashin wata kungiyar da ake kira Re-elect Buhari Movement (RBM), ya bayyana bukatar da ake akwai ta ‘yan jam’iyyar PDP su hada kai da shugaban kasa Muhammadu Buhari don samar da cigaban kasa.

A cikin hirar, Emmanual yayi magana kan karuwar yawan laifuffuka da sukar da ‘yan jam’iyyar PDP suke yi wa Buhari.

Da aka tambaye shi cewa shin ko ‘yan siyasar na iya karbar makaman da suka ba ‘yan bangar, sai yace “amsa ita ce a’a. Saboda haka yawan karuwar laifuffukan garkuwa da mutane da fashi da makamai ya zama tilas. Mun san cewa mafiyawancin ‘yan siyasar Najeriya ba su damu da makomar kasar nan ba, kansu ne kawai suka sani. Yadda za su cika aljihunsu da dukiyar da aka kebe don cigaban kasa, a gaskiya ni ban mamakin karuwar laifuffuka a wannan kasa ”

KU KARANTA: Atiku zai ci gaba da zama Shugaban kasa a zukatan yan Najeriya koda ya fadi - Showunmi

"A lokuttan da suka wuce, saboda hankalin ‘yan siyasar na wurin yadda za su shirya kansu a cikin jam’iyyunsu. Amma da yake yanzu zabe ya wuce da ‘yan siyasar da suka ci zabe da wadanda ba su ci ba duk sun samar da makamai ga ‘yan bangarsu, kuma ba su iya karbar makaman daga hannuwansu.”

"Saboda hankalin ‘yan siyasar na wurin yadda za su shirya kansu a cikin jam’iyyunsu. Amma da yake yanzu zabe ya wuce da ‘yan siyasar da suka ci zabe da wadanda ba su ci ba duk sun samar da makamai ga ‘yan bangarsu, kuma ba su iya karbar makaman daga hannuwansu.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel