Atiku zai ci gaba da zama Shugaban kasa a zukatan yan Najeriya koda ya fadi - Showunmi

Atiku zai ci gaba da zama Shugaban kasa a zukatan yan Najeriya koda ya fadi - Showunmi

- Segun Showunmi yace Atiku Abubakar zai amshi hukuncin kotun zaben Shugaban kasa game da zaben da aka yi

- Showunmi ya bayyana cewa Atiku yayi alkawarin cewa ba zai bari Najeryata sake fuskantar kowani rikici ko tashin hankali daga kayen da ya sha a zabe ba

- Hadimin yace koda da Atiku yayi imanin cewa zai samu yancinsa, shine Shugaban kasa a zukatan yan Najeriya

Atiku Abubakar dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, zai amince da hukuncin kotun zabe game da karar da ya shigar, hadimins,Segun Showunmi ya bayyana.

Ya kara da cewa, sai dai akwai alamu da ke nuna cewa Atiku zai samu yancinsa.

Karar da yashigar na kalbalantar sanar da Shugaban kasaMuhammadu Buhari a matsayin wanda ya lase zabe wada hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) tayi.

Atiku zai ci gaba da zama Shugaban kasa a zukatan yan Najeriya koda ya fadi - Showunmi

Atiku zai ci gaba da zama Shugaban kasa a zukatan yan Najeriya koda ya fadi - Showunmi
Source: UGC

Showunmi yace Atiku yayi alkawarin cewa ba zai bari Najeryata sake fuskantar kowani rikici ko tashin hankali daga kayen da ya sha a zabe ba.

KU KARANTA KUMA: Raba masarautar Kano, raba jama’a Kano ne har abada - Gumi (bidiyo)

Tsohon mataimakin Shugaban kasar, a cewar hadiminsa, ya fi son sabonta abubuwan da za su kawo cig an kasar.

Daily Trust ta ruwaito cewa Showunmi, wanda yayi Magana a wani hiran manema labarai a Abuja, ya nuna yakinin cewa hukuncin kotun zaben zai yiwa ubangidan nasa adalci duba ga tsarin kwarewar alkalan.

Ya yi watsi da ikirarin wasu mutane na cewa Atiku na da goyon bayan wasu masu ji da mulki a kasashen waje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel