Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Kansila a jahar Taraba

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Kansila a jahar Taraba

Wasu gungun yan bindiga sun yi awon gaba da wani mashahurin dan siyasa mai rike da mukamin Kansila a jahar Taraba, Daniel Ayuba, wanda ke shugabantar mazabar Sarkin Dutse dake karamar hukumar Ardo-Kola dake jahar Taraba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu abokai da makwabtan Ayuba suna cewa da tsakar daren Alhamis, 9 ga watan Mayu ne yan bindigan suka far ma Daniel a gidansa, amma wasu gungun matasa dauke da kwari da baka suka yi kokarin fatattakarsu.

KU KARANTA: An gano gawarwakin Hausawa yan canjin dala da aka kashe a jahar Legas

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Kansila a jahar Taraba

Daniel
Source: UGC

Sai dai yan bindigan sun bude wuta a sama, wanda hakan ya tsoratar da matasan, inda dukkaninsu suka ranta ana kare, a sanadiyyar haka wasu da dama daga cikinsu suka samu rauni a jikkunansu, daga nan ne kuma yan bindigan suka yi awon gaba da Kansila Daniel Ayuba.

“Wannan lamari ya zaburar damu da kowa ya kare kansa, zamu yi iya kokarinmu don ganin mun kare mutuncin kanmu daga sharrin makiya musamman duba da cewa gwamnati ta zama kuliyar barira bata cizo bata kama bera.” Inji su.

Sai dai wasu mazauna yankin sun bayyana kaduwarsu da yadda yan bindigan suka tsallake dukkanin shingen binciken ababen hawan dake yankin har suka isa gidan Kansilan, hakan tasa wasu ke zargin akwai hadin baki tsakanin wasu jami’an tsaro da yan bindigan.

A wani labari kuma, kungiyar Musulman Najeriya dake karkashin jagorancin Sarakunan gargajiya Musulmai, Jama’tu Nasril Islam ta koka kan yadda lamarin tsaro ya tabarbare a Arewacin Najeriya dama sauran sassan Najeriya gaba daya.

Sakataren JNI, Sheikh Khalid Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar daya fitar a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu, inda yace akwai bukatar shuwagabanni a dukkanin matakai su dage wajen yunkurawa domin share ma jama’ansu hawaye.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel