An gano gawarwakin Hausawa yan canjin dala da aka kashe a jahar Legas

An gano gawarwakin Hausawa yan canjin dala da aka kashe a jahar Legas

Rundunar Yansandan jahar Legas ta sanar da gano gawarwakin wasu Hausawa guda hudu masu sana’ar canjin dala da aka kashe, a cikin wani matattara tara kashi dake unguwar Ikorodu ta jahar Legas, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito rundunar Yansandan ta bayyana cewa wasu yan damfara ne suka kashe mutanen hudu bayan sun damfaresu makudan kudade a ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2019, inji kaakakin Yansandan jahar, DSP Bala Elkana.

KU KARANTA: EFCC ta cafke dan majalisa akan laifin damfara Malaman makaranta naira miliyan 4

Kaakakin yace “A ranar 4 ga watan Maris aka kai ma Yansanda rahoton cewa wasu mutane da ba’a san ko su wanene ba sun tunkari ALhaji Yakubu Musa da Alhaji Hassan Umaru akan cewa wani dan uwansu ya dawo daga kasar waje kuma yana so ya canza dala dubu goma ($10,000).

“Da farko dai sun nemi a biyasu kudin ta banki a Ikorodu, amma isarsu bankin keda wuya sai suka yi awon gaba da yan canjin zuwa wani wuri na daban, daga nan suka fara kiran yan uwansu a waya suna neman a biyasu kudin fansa kafin su sakesu.

“Daga bisani an samu an biyasu naira miliyan daya da dubu dari shida (N1,600,000) amma miyagun suka ki sakinsu, sa’annan suka kashe wayoyinsu, tun daga wancan lokaci ba’a kara ji daga garesu ba. Hakan ne yasa kwamishinan Yansandan jahar, Zubairu Muazu ya umarci Yansandan SARS su fara gudanar da bincike da nufin ceto mutanen.

“Wannan bincike ya gudana ne a karkashin jagoranicin SP Godfrey Soriwei, wanda ya kama mutane uku, Oluwatosin Olanrewaju, Mayowa Olawuni da Babatunde Idris, kuma dukkaninsu sun tabbatar da hannayensu cikin kisan yan canjin, sa’annan suka jagoranci Yansandan zuwa mabuyarsu inda suka jefa gawarwakin yan canjin.” Inji shi.

Kaakakin yace sun gano bindigu guda biyar da alburusai da dama, adda, gatari da kayan tsafe tsafe, kuma sun ce gawarwaki guda biyu na yan canjin ne, yayin da sauran gawarwaki guda biyun kuma na wasu abokan hamayyarsu ne yan kungiyar asiri da suka kashe suka jefar.

Daga karshe kaakakin yace rundunar zata gurfanar da miyagun gaban kotu don fuskantar hukuncin daya dace dasu da zarar ta kammala gudanar da binciken kwakwaf akansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel