Dalibin Sakandare ya kashe abokinsa akan budurwa a jihar Katsina

Dalibin Sakandare ya kashe abokinsa akan budurwa a jihar Katsina

- Son zuciya da soyayya sun ja wani dalibin makarantar sakandare a jihar Katsina kashe wani abokinsa akan budurwa da sabani ya shiga tsakaninsu a kanta

- Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, kuma yanzu haka yana kotu domin hukunta shi

Wani dalibi mai shekaru 18, Ahmed Abubakar, dake makarantar Government Secondary School Katsina, a cikin jihar Katsina, an kama shi da laifin kashe wani dalibi abokinsa, mai suna Mikailu Mustapha, bayan sun samu sabani a tsakanin su akan wata budurwa da suke so.

Hukumar 'yan sanda ta ce Abubakar wanda aka fi sani da Sha'aban, ya kashe Mustapha abokinsa ta hanyar amfani da wuka a lokacin da suka samu sabani tsakaninsu, hukumar ta kara da cewa Sha'aban ya amsa laifin na sa.

Dalibin Sakandare ya kashe abokinsa akan budurwa a jihar Katsina

Dalibin Sakandare ya kashe abokinsa akan budurwa a jihar Katsina
Source: Depositphotos

Sakamakon haka, an kai shi gaban kotun Majistare ta jihar Katsina da laifin aikata kisan kai karkashin sashe na 221 na dokar kasa.

Mai gabatar da kara, ASP Sani Ado, ya shaidawa kotu ranar Alhamis cewa hukumar su ta na cigaba da gabatar da bincike.

Alkalin kotun, Mai Shari'a Hajiya Fadile Dikko, ta daga sauraron karar har zuwa 11 ga watan Yuni, inda ta bukaci a sanya wanda ake tuhumar a gidan yari.

KU KARANTA: 'Yan bindiga suna karbar haraji a hannun manoma kafin su basu damar shiga gonakin su

A wani rahoto da ya yi kama da wannan, wani dalibin Jami'ar Dutsinma mai shekaru 20 a duniya, Sani Anas, shima yana fuskantar kotu akan zargin kama shi da aka yi da bindiga.

An caje shi a karkashin sashe na 3 na dokar fashi da makami da kuma sashe na 319A na dokar kasa.

Hakazalika shi ma Anas an tsare shi a gidan yari har zuwa ranar 13 ga watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel