'Yan bindiga suna karbar haraji a hannun manoma kafin su basu damar shiga gonakin su

'Yan bindiga suna karbar haraji a hannun manoma kafin su basu damar shiga gonakin su

- Manoma a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun koka akan yadda 'yan bindiga ke karbar haraji a hannunsu kafin su basu damar shiga gonakin su domin gabatar da aiki a wannan daminar

- Rahotanni sun nuna cewa kimanin manoman shinkafa 350 ne suka bar gonakin su saboda matsalar rashin tsaron a yankin

Manoma a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana yadda suke cikin mummunan tashin hankali sanadiyyar sace sacen mutane, sun bayyana cewa 'yan bindiga suna karbar haraji a wurinsu kafin su basu damar shiga gonakinsu.

Sun ce bayan haka, yawancin su an tilasta musu barin gonakin su, inda suka kara cewa matsalar baza ta kau ba har sai an dauki matakan gaggawa akan 'yan bindiga dake addabar yankin nasu; sun kuma kara da cewa muddin ba a dauki mataki ba matsalar karancin abinci za ta kunno kai a fadin kasar nan.

'Yan bindiga suna karbar haraji a hannun manoma kafin su basu damar shiga gonakin su

'Yan bindiga suna karbar haraji a hannun manoma kafin su basu damar shiga gonakin su
Source: Twitter

Misali a jihar Zamfara, kungiyoyin manoma sun ce 'yan bindiga sun koma karbar haraji a hannunsu kafin su basu damar shiga gonakin su.

Kungiyoyin sun bayyana cewa, a jihar Kebbi, kimanin manoman shinkafa 350 ne suka bar gonakin su saboda matsalar tsaron.

Don haka, sun yi gargadi cewa matsalar 'yan bindiga da garkuwa da mutane a yankin arewa maso yamman zai iya janyo matsalar karancin abinci a yankin da kashi 50 cikin 100.

KU KARANTA: An kama wadanda ke da hannu a sace Hakimin Daura

Shugabannin kungiyoyin manoman na Najeriya da kuma kungiyoyin masu noman shinkafa na Najeriya, a tattaunawar da suka yi da manema labarai sun bayyana matsalolin da kungiyoyin suke fuskanta akan matsalar tsaron.

Hakazalika kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa kimanin gidaje dubu goma ne, wadanda mafi yawancin su manoma ne, aka tilastawa barin gidajen su a jihar Zamfara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel