Wani sanata ya lashi takobin fada da bude sabbin jami'o'i a Najeriya

Wani sanata ya lashi takobin fada da bude sabbin jami'o'i a Najeriya

-Sanata Adeyeye ya lashi takobin fada da bude sabbin jami'o'i a Najeriya idan har ba'a inganta wadanda ke kasar ba a yanzu.

-Sake bude sabbin jami'o'in ba tareda da inganta tsoffin ba tamkar damfara ce ga yaranmu, inji sanatan.

Sanata Olusola Adeyeye a ranar Alhamis yace zai cigaba da kalubalantar kudurin sake bude sabbin jami’o’i a Najeriya.

Adeyeye yayi wannan furucin ne yayinda yake tofa albarkacin bakinsa game da muhawara da ta gudana a majalisar dattawa kan bude jami’ar Maritime a Lokaja, jihar Kogi.

Wani sanata ya lashi takobin fada da bude sabbin jami'o'i a Najeriya

Sanata Olusola Adeyeye
Source: UGC

KU KARANTA:Dalibai sunyi zanga-zanga kan cire shugaban jami’ar Kwara

Wannan kudurin ya fito ne daga hannun sanata Isaac Alfa mai wakiltar Kogi ta gabas. A lokacinda Adeyeye yake tsokaci akan wannan kuduri cewa yayi tsoffin jami’o’in dake garemu basu samun kulawar da ta dace.

Haka kuma, ya lashi takobin cigaba da fada da wannan kuduri na bude sabbin jami’o’i har sai an inganta wadanda muke dasu a halin yanzu ta hanyar zuba isassun kudi cikin ayyukan jami’o’in.

“ Babu abin boyewa cikin lamuran jami’o’in kasar nan, kowa yasan basu samun kulawar da ta dace. Ana cikin wannan halin ne za’a dauke wasu makudan kudade a sake bude wasu jami’o’in. Wanda yin hakan zai kara zamewa gwamnati nauyi da kuma karuwar kashe kudi.

“ Ni bazan taba amincewa da kuduri bude sabbin jami’o’i ba har sai an inganta tsoffin da muke dasu a wannan kasa tamu. In kuwa ba’ayi hakan ba zan iya cewa muna damfarar diyanmu ne kawai da kanmu.

“ Idan har akwai bukatar jami’ar karatun Maritime, to me zai hana aje sassan dake da ruwa a kasar nan cikin jami’o’insu a bude sashen koyar da irin wannan ilimin na Maritime. Amma bude sabbi a wannan lokaci bashi bane abu mafi a’ala". A cewar sanata Adeyeye.

Wannan furucin nashi ya samu goyon bayan sanata Adamu Aliero, inda ya mara masa baya akan duk abinda ya fadi. Jami’o’in Najeriya na bukatar gyara kafin azo maganar kirkirarar sabbi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel