Su daure mu idan mun yi sata - Gwamnan APC mai barin gado

Su daure mu idan mun yi sata - Gwamnan APC mai barin gado

Gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo ya ce baya fargabar da wata bincike da za a yiwa gwamnatinsa bayan ya sauka daga mulki.

Gwamnan ya furta hakan ne a ranar Alhamis a jawabin da ya yi wurin taron da Cibiyar Zaman Lafiya ta shirya a dakin taro na Subomi Balogun da ke Jami'ar Ibadan.

Wadanda suka hallarci taron sun hada da manyan jami'an gwamnati da shugabanin hukumomin tsaro.

Su daure mu idan mun yi sata - Gwamnan APC mai barin gado

Su daure mu idan mun yi sata - Gwamnan APC mai barin gado
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: An tura 'zauna gari banza' gidan yari saboda taba nonon kwaila

"Za mu cigaba da aiki har zuwa ranar da wa'adin mu za ta kare. Bamu damu da jita-jitar da wasu ke yadawa ba. A halin yanzu da na ke magana, akwai sauran kwanaki 18 kafin wa'adin mulki na ya kare," inji shi.

"Idan sun hau mulk, suna iya soke dukkan kwangilolin da muka rattaba hannu a kai. Su gudanar da dukkan binciken da za suyi kuma idan munyi sata sai su kama mu."

A cikin watan Maris ne zababen gwamna mai jiran gado, Seyi Makinde ya zargi Ajimobi da saka hannu a kan kwangilolin da kudinsu ya kai Naira biliyan 30 a rana guda.

Ya dau alwashin bibiyar dukkan kwangilolin da gwamnan mai barin gado ya ratabba hannu a kai da zarar ya dare kujerar mulki.

Sai dai Ajimobi ya shaidawa mahalarta taron a ranar Alhamis cewa gwamnatinsa da samu nasarori sosai wadda hakan ya kawo cigaba a jihar.

Ya ce daya daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu shine kafa kwamitin kula da makarantu (SGB).

"SGB da muka kirkiro ya samar da nasarori a jarabawar makarantun sakandire a jihar mu. A yau, jihar mu ce kan gaba a jarabawar WASSCE a shekaru 18 da suka gabata," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel