Shugabancin majalisa: Sanatocin PDP da dama suna goyon baya na - Lawan

Shugabancin majalisa: Sanatocin PDP da dama suna goyon baya na - Lawan

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce akwai sanatocin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) masu yawa da ke goyon bayan takararsa na shugabancin majalisar dattawa.

A hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Alhamis a Abuja, Lawan ya yi alkawarin cewa ba zai bawa abokan aikinsa kunya ba muddin suka zabe shi.

Lawan ya samu goyon baya daga shugabanin jam'iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) har da da shugaba Muhammadu Buhari sai dai hakan bai hana wasu daga cikin abokan aikinsa daga bangaren Arewa maso Gabas neman takarar kujerar ba.

Shugabancin majalisa: Sanatocin PDP da dama suna goyon baya na - Lawan

Shugabancin majalisa: Sanatocin PDP da dama suna goyon baya na - Lawan
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An tura 'zauna gari banza' gidan yari saboda taba nonon kwaila

Amma Lawan ya ce kwakwata baya damuwa saboda wasu daga yankinsa suna neman kujerar shugabancin majalisar. Mutane biyun daga Arewa maso gabas da ke neman shugabancin majalisar sune Ali Ndume da Danjuma Goje.

"Na tattauna da mafi yawancin sanatocin APC kuma duk suna tare da mu," inji shi.

"Mafi yawancin sanatocin PDP suna goyon baya na har da sanatan YPP, Sanata Ifeanyi Uba daga jihar Anambra shima yana tare da mu.

"Muna zuwa gida-gida; muna tattaunawa da zababun sanatoci. Munyi magana da sanatocin APC da PDP da YPP saboda muna fatan duk za muyi aiki tare a nan gaba.

"Ina son in tabbatarwa kowa cewa nayi imanin cewa zan iya daukan wannan nauyin. Da taimakon Allah da kuma hadin kan sanatocin APC, PDP da YPP a majalisar, zamu sauke nauyin da za a daura mana.

"Bana gaba da sauran sanatocin yanki na da suke takara da ni duk da cewa jam'iyyar mu ta goyi baya na, hakan baya nufin sauran ba za su iya aikin ba sai dai shugabanin jam'iyyar mu sun san abinda suka hango har yasa suka goyi baya na."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel