Abinda Buhari ya fada wa shugabannin hukumomin tsaro

Abinda Buhari ya fada wa shugabannin hukumomin tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin hukumomin tsaro da su kara zage dantse domin kawo karshen kalubalen tsaro dake damun sassan kasar nan.

Da yake magana da shugabannin hukumomin tsaro yayin ganawar su a ranar Alhamis, shugaba Buhari ya fada musu cewar akwai bukatar 'yan Najeriya suke bacci da idonsu biyu a rufe, cikin kwanciyar hankali.

Ibok Ekwe Ibas, shugaban rundunar sojojin ruwa, ne ya bayyana hakan yayin gana wa da manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala ganawar su da Buhari da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Alhamis.

"Babban dalilin ganawar shine domin sanar da shugaban kasa halin da kasa ke ciki dangane da harkarvtsaro bayan kammala hutun kwana 10 da ya yi a kasar Ingila.

Abinda Buhari ya fada wa shugabannin hukumomin tsaro

Buhari da shugabannin hukumomin tsaro
Source: Facebook

"Shugabannin hukumomin tsaro sun sanar da shi abinda ke faruwa, musamman a bangaren yaduwar kananan makamai a hannun farar hula da irin kokarin da hukumomin tsaro ke yi domin dakile matsalolin da hakan ke haifar wa.

DUBA WANNAN: Gwamnan CBN: Majalisar dattijai ta karanta wasikar Buhari

"Ya bamu umarnin cewar mu yi iya bakin kokarin mu domin tabbatar da cewar 'yan Najeriya sun kwanta bacci sun tashi cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar matsalar rashin tsaro ba," a cewar sa.

A ranar Alhamis ne shugaba Buhari ya sake ganawa da shugabannin hukumomin tsaro a karo na biyu bayan dawowar sa daga hutun kwana 10 da ya yi a kasar Ingila.

Sun fara ganawar ne da misain karfe 11:00 na safe, wacce ta kai su har karfe 3:00 na rana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel