Shugabancin majalisa: Kungiyar arewa sun gudanar da gangami don goyon bayan Goje

Shugabancin majalisa: Kungiyar arewa sun gudanar da gangami don goyon bayan Goje

Kungiyar matasan arewa reshe Arewa maso Yamma (CNYO), a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu ta gudanar da taro a Kaduna sannan tayi kira ga Sanata Danjuma Goje da ya bayyana ra’ayinsa na neman shugabancin majalisar dattawa.

Matasan wadanda suka yi tattaki a titunan Kaduna, sun bayyana Sanata Goje a matsayin sanata mafi cancanta wajen rikon mukamin shugabancin majalisa daga yankin arewa maso gabashin kasar.

Yayin da yake magana a taron, shugaban kungiyar, Injiniya Hassan Idris yace kungiyar baza ta amince da duk wani dan takara ba daga yankin Arewa maso Gabashin kasar sai dai Goje shi kadai.

Idris ya bayyana Sanata Goje a matsayin mafi cancantan kuma wanda ke shirye a yakin neman ofishin shugaban majalisar fiye da sauran yan takaran.

Shugabancin majalisa: Kungiyar arewa sun gudanar da gangami don goyon bayan Goje

Shugabancin majalisa: Kungiyar arewa sun gudanar da gangami don goyon bayan Goje
Source: Depositphotos

Shugaban wanda ya mika wasikar akan matsayin kungiyar ga jami’in All Progressives Congress (APC) reshen Arewa maso Yamma yace shawaransu akan mara ma Sanata Goje baya ya kasance bisa ra’ayin damokardiyya wanda ya ba kungiyar daman bayyana matsayin ta ga babban sakataren jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sanusi ya samu mukami a majalisar dinkin duniya kwana daya bayan an kacaccala masarautarsa

A martanin shi bayan karban wasikan, hadimin sakataren APC reshen Arewa maso Yamma, Mallam Suleiman Adamu ya fada ma kungiyan cewa za a gabatar da wasikar su zuwa ga babban Sakataren kasa don daukan matakin da take bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel