Gwamnatin Plateau za ta rushe da kuma kone babbar kasuwar Jos a ranar 19 ga Mayu

Gwamnatin Plateau za ta rushe da kuma kone babbar kasuwar Jos a ranar 19 ga Mayu

Gwamnatin jihar Plateau ta sanya ranar da za ta rushe tare da kona wani sashi na kasuwar Jos, babbar birnin jihar. Ta zabi ranar 19 ga watan Mayu domin cika wannan aiki, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Kwashinan labarai na jihar, Yakubu Datti ne ya bayar da sannarwar kamar yadda majiyarmu ta ruwito.

Sanarwar ta kuma shawarci wadanda ke zaune a mita 200 daga kasuwar da su gaggauta ficewa nan da ranar 17 ga watan Mayu kafin karfe 6:00 na yamma.

“Za a hana zirga-zirgar ababen hawa a dukkan hanyoyin da suka doshi kasuwar, kuma za a rufe su, saboda tabbatar da tsaron rakuya da dukiyoyin jama’a.

Gwamnatin Plateau za ta rushe da kuma kone babbar kasuwar Jos a ranar 19 ga Mayu

Gwamnatin Plateau za ta rushe da kuma kone babbar kasuwar Jos a ranar 19 ga Mayu
Source: Depositphotos

“Gwamnati na bada hakuri kan duk wata takuwarawa da jama’a za su fuskanta sakamakon wannan gagarimin aiki da za a yi,” inji Datti.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sanusi ya samu mukami a majalisar dinkin duniya kwana daya bayan an kacaccala masarautarsa

Ya kuma kara jaddada kudirin Gwamna Simon Laong na ganin ya sake gina babbar Kasuwar ta Jos.

Datti ya kara jadadda cewa gwamnati na ci gaba da daukar dukkan wasu matakai da suka wajaba, domin ganin an sake gina kasuwar a cikin yanayin da jama’a ba su tagayyara ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel