Da kun hangi Ministan kwadago ku kai ma sa farmaki - Kungiyar kwadago ta gargadi 'ya'yan ta

Da kun hangi Ministan kwadago ku kai ma sa farmaki - Kungiyar kwadago ta gargadi 'ya'yan ta

Kungiyar kwadago ta Najeriya a ranar Alhamis ta dauki sulke na yakar Ministan kwadago na kasa, Dakta Chris Ngige, biyo bayan farmakin da aka kaiwa ‘ya’yan ta yayin zanga-zangar da suka gudanar a harabar gidan sa da ke garin Abuja.

‘Yan baranda sun kai hari kan mambobin kungiyar kwadago yayin zanga-zangar lumana da suka gudanar a harabar gidan Ministan da ke garin Abuja a ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2019.

Kungiyar cikin fushi yayin yunkurin ta ramawa kura aniyya, ta umurci 'ya'yan ta a kan kada su ragawa Ministan wajen kai ma sa farmaki tare da dukkanin ahalin sa a yayin da suka yi idanu hudu da su a ko ina cikin fadin kasar nan.

Da kun hangi Ministan kwadago ku kai ma sa farmaki - Kungiyar kwadago ta gargadi 'ya'yan ta

Da kun hangi Ministan kwadago ku kai ma sa farmaki - Kungiyar kwadago ta gargadi 'ya'yan ta
Source: Depositphotos

Yayin da tuni ta mika koken ta gaban kungiyoyin kwadago na nan gida da kuma na duniya baki daya, shugaban kungiyar Ayuba Wabba yayin ganawarsa da manema labarai, ya gindaya umurni ga mambobin kungiyar a kan nuna babu sani babu sabo a yayin kacibus da Ministan na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KARANTA KUMA: Gwamna Masari ya ware N200m domin yakar bahaya a fili cikin jihar Katsina

A yayin da a ranar Litinin ta mako mai zuwa za gudanar da wata zanga-zangar a garin Abuja, Kungiyar ta ce ba za ta lamunci wannan cin kashi na Dakta Ngige ba sakamakon dakilewa ma’aikata ‘yancin gudanar da zanga-zanga domin neman biyan bukatu gwargwadon tanadi na hakki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel