Gwamna Masari ya ware N200m domin yakar bahaya a fili cikin jihar Katsina

Gwamna Masari ya ware N200m domin yakar bahaya a fili cikin jihar Katsina

Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ruwaito, matsalar yin bahaya a filin Allah na ci gaba da kasancewa babbar barazanar tsafta musamman a kasashe masu tasowa da kuma nakasun ci gaba kamar Najeriya da ire-iren ta.

A wurare da dama na yankunan karkara har ma dai cikin wasu birane fadin kasar nan, wasu mutane kan yi bahaya a waje a sanadiyar rashin makewayi ba tare da la'akari da illar hakan ka iya shafar lafiyar al'umma ba.

Wani kiyasi da reshen lafiya na majalisar dinkin duniya ya haskaka cewa, Najeriya ta kasance kasa ta daya a Afirka, haka kuma ta kasance kasa ta biyu a duniya cikin jerin kasashe masu fama da matsalar yin bahaya a waje.

Gwamna Masari ya ware N200m domin yakar bahaya a fili cikin jihar Katsina

Gwamna Masari ya ware N200m domin yakar bahaya a fili cikin jihar Katsina
Source: UGC

A sanadiyar wannan kalubale, mun samu cewa gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya shirya bayar da bashin Naira miliyan dari biyu domin gina bandakuna da wuraren tsugunno a gidajen al'umma masu karamin karfi domin kawo karshen yin bahaya a sararin Allah.

Gwamnatin jihar Katsina ta daura damarar inganta tsaftace muhallai da kuma kare lafiyar al'umma ta hanyar samar da bandakunan bahaya kamar yadda shugaban cibiyar raya karkara da tsaftar muhallai a jihar ya bayyana, Alhaji Aminu Dayyabu.

KARANTA KUMA: 'Yan sanda sun cafke mutane 8 da ake zargi da laifin kisan kai a garin Abuja

Ya yi bayanin cewa tun a yanzu gwamnatin jihar ta bayar da Naira Miliyan hamsin somin tabi na farar da wannan aiki gadan-gadan domin muhimmancin kare lafiyar al'ummar ta. Ya ce aikin gina wuraren kewayawa da kuma bahaya zai gudana cikin kananan hukumomi 9 da ke fadin jihar.

A yayin da kowane magidanci zai samu tallafin Naira dubu arba'in domin gina makiwayi a muhallin sa, Alhaji Dayyabu ya ce kananan hukumomin sun hadar da Dutsin-Ma, Safana, Batagarawa, Kaita, Rimi, Bakori, Faskari, Mai'adua da kuma Sandamu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel