An kama wadanda ke da hannu a sace Hakimin Daura

An kama wadanda ke da hannu a sace Hakimin Daura

- Dubun barayin da suka sace Magajin Garin Daura ta cika, inda hukumomin tsaron kasar nan suka kama wasu wanda ake zargin suna da hannu a sace hakimin

- Yau dai kwana takwas kenan har yanzu ba a samu labarin halin da hakimin yake ciki ba

An kama wadanda ake zargin sun sace sirikin babban dogarin shugaba Buhari, Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba.

Babban hafsan sojojin ruwa, Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas shi ne ya bayyana hakan a karshen taron da aka gabatar na shugabannin tsaro a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis din nan.

Membobin kwamitin tsaron da suka halarci taron sun hada da: Babban hafsan tsaro na soji, General Gabriel Olonisakin, Babban hafsan rundunar sojin Najeriya, Lt. Gen. Tukur Buratai, Babban hafsan sojin ruwa, Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas da kuma Babban hafsan sojin sama, Air Marshall Abubakar Sadique.

An kama wadanda ke da hannu a sace Hakimin Daura

An kama wadanda ke da hannu a sace Hakimin Daura
Source: UGC

Sauran mutanen da suka samu halartar taron sun hada da: Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; Mai bawa shugaban kasa shawara a fannin tsaro, Babagana Monguno; Ministan tsaro, Mansur Dan Ali; Darakta janar na hukumar leken asiri (NIA), Ahmed Abubakar; Shugaban hukumar 'yan sanda na kasa, Mohammed Adamu da kuma Darakta janar na hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi.

KU KARANTA: Abubuwa masu muhimmanci da gwamnan babban banki ya kawo Najeriya

Ibas wanda ya yi magana a madadin takwarorinsa, ya shaidawa manema labarai cewa, nan ba da dadewa ba za a hukunta masu laifin.

"An yi kokari sosai, an kama wadanda ake zargin sun sace Hakimin Daura, kuma nan ba da dadewa ba za a hukunta," in ji shi.

Uba wanda ya ke da mukamin Magajin Garin Daura, an sace shi ranar Laraba 1 ga watan Mayu, 2019, a gidan shi dake garin Daura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel