Gwamnan CBN: Majalisar dattijai ta karanta wasikar Buhari

Gwamnan CBN: Majalisar dattijai ta karanta wasikar Buhari

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya karbi wasikar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika ta neman tabbatar da sabunta nadin Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) a karo na biyu.

Saraki ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aike a zauren majalisa ranar Alhamis.

Wasikar mai taken 'sabunta nadin Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya' ta isa ofishin shugaban majalisar dattijai a ranar 9 ga watan Mayu, 2019.

Wasikar ta ce: "bayan karewar wa'adin mulkin gwamnan babban bankin Najeriya a ranar 2 ga watan Yuni, 2019, bisa la'akari da sashe na 8 (1) da sashe na (2) na kundin dokokin babban bankin kasa na shekarar 2007, ina gabatar muku da Godwin Emefiele domin amincewa da nadinsa a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya da zai sake shugabantar bankin na tsawon shekaru biyar a karo na biyu.

Gwamnan CBN: Majalisar dattijai ta karanta wasikar Buhari

Gwamnan CBN: Godwin Emefiele
Source: Depositphotos

"Ina fatan mambobin majalisar dattijai masu girma zasu duba tare da tabbatar da zabinsa ba tare da bata lokaci ba.

DUBA WANNAN: Yadda muka kama Mohammed Khalid a Najeriya - Kasar Amurka

Sai dai, majalisar ba ta tsayar da ranar da zata duba wannan bukata tare da tabbatar da zabin Emefiele da shugaba Buhari ya sake yi ba.

Tsohon shugaban kasa Jonathan ne ya fara nada Emefiele a matsayin gwamnan CBN a karshen zangon mulkinsa.

Kafin nada shi a matsayin gwamnan CBN, Emefile ya shafe tsawon shekaru 26 ya na aiki a bankuna masu zaman kansu, inda har ya kai ga babban darektan gudanarwa a bankin Zenith.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel