Abubuwa masu muhimmanci da gwamnan babban banki ya kawo Najeriya

Abubuwa masu muhimmanci da gwamnan babban banki ya kawo Najeriya

An bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya tura sunan Godwin Emefiele zuwa ga majalisar dokoki domin sake bashi mukamin gwamnan babban banki a karo na biyu

Wasu shaidu a fadar shugaban kasa da CBN, wadanda suka bukaci a sakaye sunansu, sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a yau Alhamis dinnan cewa shugaba Buhari ya gabatar da sunan gwamnan ga majalisar dokokin kasar nan domin ta sanya hannu.

Godwin Emefiele wanda shi ne gwamnan babban bankin Najeriya na 11, ya fara aikin sa ranar 3 ga watan Yuni, 2014, inda zai kammala aikin nasa nan da wata daya mai zuwa.

Emefiele ya zama gwamnan babban bankin a lokacin da darajar naira ta fadi a kasashen duniya.

Abubuwa masu muhimmanci da gwamnan babban banki ya kawo Najeriya

Abubuwa masu muhimmanci da gwamnan babban banki ya kawo Najeriya
Source: Depositphotos

A jawabin da yayi a wani taron manema labarai, gwamnan ya bayyana burinsa na gyara babban bankin Najeriya domin al'umma, wanda zai dawo da darajar naira da kuma inganta cigaban tattalin arziki.

A cikin shekaru biyar din da yayi, Emefiele ya gabatar da manufofi da yawa wadanda masana tattalin arziki su ka dinga sukar shi a kai.

Wasu manyan manufofi da bankin ya gudanar a cikin shekaru biyar sun hada da shirin Anchor Borrowers (ABP) wanda aka shirya domin kara yawan kayan abinci na gida.

Babban bankin kuma ya yanke shawarar dakatar da abubuwa 41 daga samun damar canji na kasashen waje, domin taimakawa wajen cigaban masana'antu na gida.

KU KARANTA: Jerin kasashe 25 da suke da karfin tattalin arziki a duniya

Har ila yau, a 2018, Babban Bankin CBN ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tsabar kudi dala biliyan 2.5, inda suka yi da kasar China.

An tsara yarjejeniyar kudin ne saboda taimakawa wajen cinikayya tsakanin kasar Sin da Najeriya da kuma rage darajar dalar Amurka a matsayin kudin cinikayya na kasar.

Babban bankin tare da hadin gwiwar bankunan Najeriya, sun kaddamar da tsarin tantance mutane, wanda aka sanyawa suna "Bank Verification Number (BVN)" a turance.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel