'Yan sanda sun cafke mutane 8 da ake zargi da laifin kisan kai a garin Abuja

'Yan sanda sun cafke mutane 8 da ake zargi da laifin kisan kai a garin Abuja

Hukumar 'yan sandan Najeriya a reshen ta dake Abuja, ta samu nasarar cafke akalla Mutane takwas da ake zargin hannun su cikin kisan wata mata mazauniyar garin Abuja, Esther Okah, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

'Yan sanda sun cafke mutane 8 da ake zargi da laifin kisan kai a garin Abuja

'Yan sanda sun cafke mutane 8 da ake zargi da laifin kisan kai a garin Abuja
Source: UGC

Esther ta yi gamo da ajali yayin da masu mummunar ta'ada su ka sheke ta ta hanyar suka da makami a yankin Unguwar Siminti ta gundumar Gwarimpa yayin da ta ke kan hanyar dawowa daga yawon shakatawa tare da abokanai a ranar Lahadin da ta gabata.

Cikin rahoton sanarwa da kakakin 'yan sanda na garin Abuja ya gabatar a ranar Alhamis, Danjuma Gajere ya ce a halin ababe zargin takwas na ci gaba da taimakawa jami'ai wajen bankado ainihin makasan Esther.

Gajere cikin sanarwar yayin ganawa da manema labarai ya bayyana cewa, bincike ya kankama kan wannan mummunan ta'addanci wanda da zarara ya kammala ababen zargin za su amsa bayanai a gaban Kuliya domin zartar masu da hukunci daidai da abin da suka aikata.

KARANTA KUMA: Ku sadu da Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele

Kazalika kwamishinan 'yan sanda na garin Abuja, Adamu Chiroma, ya bayar da tabbacin sa ga al'ummar birnin tarayya ta jajircewa gami da tsayuwar daka wajen dakile aukuwar miyagun ababe tare da tabbatar da ingataccen tsaro.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel