Majalisar dokoki ta dakatar da shugabanin hukumomi 27 a Imo

Majalisar dokoki ta dakatar da shugabanin hukumomi 27 a Imo

- Majalisar dokokin jihar Imo ta dakatar da shugabanin kananan hukumomi 27 a jihar Imo

- Majalisar ta dauki wannan matakin ne sakamakon rashin amsa gayyatar majalisar da shugabanin kananan hukumomin

- Majalisar ta ce rashin amsa gayyatar domin bayyani kan yadda suke kashe kudadensu alama ce ta rashin da'a ga doka

Majalisar dokoki ta dakatar da dukkan shugabanin karamar hukumomi a Imo

Majalisar dokoki ta dakatar da dukkan shugabanin karamar hukumomi a Imo
Source: UGC

Kasa da sa'o'i 72 bayan gwamnatin tarayya ta bawa kananan hukumomi ikon sarrafa kudadensu, 'yan majalisar dokoki a jihar Imo sun dakkatar da dukkan zababun shugabanin kananan hukumomi 27 da ke jihar.

DUBA WANNAN: Kotun Shari'a za ta datse hannun mutum 10, a jefe 5 a Bauchi

'Yan majalisar sun dauki wannan mataki ne sakamakon rashin bayyana a gaban majalisar da shugabanin kananan hukumomin suka gaza yi domin amsa tambayoyi a kan yadda suka kashe kudaden kananan hukumominsu.

Mamba mai wakiltan mazabar Nkwerre, Chika Madumere ne ya gabatar da kudirin dakatar da shugabanin kananan hukumomin nan take kuma sauran mambobin majalisar suka goyi bayan hakan.

A cewarsa, rashin amsa gayyatar 'yan majalissun cin fuska ne da rashin girmama doka da majalisar dokokin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel