Dalibai sunyi zanga-zanga kan cire shugaban jami’ar Kwara

Dalibai sunyi zanga-zanga kan cire shugaban jami’ar Kwara

-Daliban jami'ar jihar Kwara sun nuna rashin jin dadinsu dangane da sauya masu shugaban jami'arsu da gwamnatin jihar tayi

-Masu zanga-zangar su baiwa gwamnati awa 24 da tayi masu bayanin dalilin daukar wannan hukunci ko kuma su sauya salon zanga-zangar

Kungiyar dalibai ta kasa Najeriya wato NANS a hadin guiwa da kungiyar daliban Jami’ar Kwara dake Malete, sun roki gwamnan jihar Kwara na ya dawo masu da shugaban jami’ar da aka tuge.

Gwamnan ya bada umurni a ranar Talata ga shugaban jami’ar Farfesa Abdulrasheed Na’Allah da ya mika ragamar jagoranci zuwa hannun Farfesa Kenneth Adeyemi a matsayin mai rikon kwarya, kasancewar wa’adinsa zai kare a watan Yulin 2019.

Dalibai sunyi zanga-zanga kan cire shugaban jami’ar Kwara

Dalibai sunyi zanga-zanga kan cire shugaban jami’ar Kwara
Source: Twitter

KU KARANTA:Shirun Buhari na damun mu, inji yan majalisar dokokin APC

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zanga-zangar lumana, shugaban NANS reshen jihar Kwara Saheed Olosasa tareda shugaban kungiyar dalibai na jami’ar Abdulganiyu Dikko, ya bukaci gwamnan yayi masu bayanin dalilin daukar wannan mataki cikin sa’o’i 24 ko kuma su sauya salon zanga-zangar.

A wani labarin mai kama da wannan, mun ji cewa yan jam'iyar APC dake majalisar dokoki sun nuna damuwarsu kan halin ko in kula daga wurin shugaba Buhari kan zaben shugabannin majalisar dokokin dake tafe. Shirun Buhari na damun mu, inji yan majalisar dokokin APC

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel