Badakalar kudi: Gwamnatin Kano ta titsiye hadimin Sarki Sanusi

Badakalar kudi: Gwamnatin Kano ta titsiye hadimin Sarki Sanusi

Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta gayyaci hadimin Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II domin amsa tambayoyi a kan zargin almundaha na kudade.

Isa Bayero wanda shine babban dogarin marigayi Sarki Ado Bayero ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis cewa ya amsa gayyatar Hukumar sauraron karafi da yaki da rashawa na jihar.

Hukumar yaki da rashawa na Kano ta gayyaci hadiman sarki Sanusi

Hukumar yaki da rashawa na Kano ta gayyaci hadiman sarki Sanusi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An tura 'zauna gari banza' gidan yari saboda taba nonon kwaila

Ya ce: "An mika min wasu takardu a lokacin da na bayyana a gaban kwamitin binciken, na duba takardun na bukaci a bani lokaci domin inyi nazari a kansu sannan in mayar da su.

"Ba a kayyade min lokacin da zan yi nazari in mayar da takardun ba amma idan na gama nazarin a yau zan koma gobe domin in fuskanci kwamitin domin amsa tambayoyin su."

Isa ya ce an masa tambayoyi sannan an bukaci da dawo da wasu takardu a ranar Juma'a.

Sauran mutane da kwamitin ta gayyata ba su amsa gayyatar ba - Mohammad Sani Kwaru (Akanta), Mannir Sani (Shugaban ma'aikatan fada), Danburan Mujittafa da Falakin Kano.

A jiya Laraba ne gwamna Abdullahi Ganduje ya saka hannu a kan dokar kirkirar sabbin masarautu hudu a Kano wadda wasu ke ganin mataki ne da aka dauka domin kuntatawa Mai Martaba Sarki Sanusi Lamido Sanusi II.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel