Yanzu yanzu: An bi doka yadda yakamta wurin nadin sabon shugaban hukumar NYSC, inji majalisar dattawa

Yanzu yanzu: An bi doka yadda yakamta wurin nadin sabon shugaban hukumar NYSC, inji majalisar dattawa

-Majalisar dattawa ta aminta da nadin Shuaibu Ibrahim a matsayin sabon shugaban NYSC

-Babu wani murkususu da akayi yayin nadin Shuaibu Ibrahim shugaban hukumar matasa masu yiwa kasa hidima, inji majalisar dattawa

Majalisar dattawa tace tabbas an bi doka wajen nadin sabon shugaban hukumar matasa masu yiwa kasa hidima ta NYSC wato Shuaibu Ibrahim.

Majalisar tace ta cinma matsayane bayan samun kyakkyawan rahoto daga kwamitin majalisar mai kula da al’amuran matasa da kuma wasanni wanda sanata Ogba Obinna ke jagoranta a ranar Alhamis.

Yanzu yanzu: An bi doka yadda yakamta wurin nadin sabon shugaban hukumar NYSC, inji majalisar dattawa

Yanzu yanzu: An bi doka yadda yakamta wurin nadin sabon shugaban hukumar NYSC, inji majalisar dattawa
Source: UGC

KU KARANTA:Shirun Buhari na damun mu, inji yan majalisar dokokin APC

Rahoton mai taken, ‘Bincike akan nadin sabon shugaban hukumar NYSC daga shugaban hafsun soji Najeriya.’ Bayan kammala nata binciken kwamitin ya kawo rahoto gaban majalisar dattawa inda aka tabbatar da sahihancin nadin a ranar Alhamis.

Za’a iya tunawa a ranar 26 ga watan Afrilu ne hukamar sojin Najeriya ta sanar da Shuaibu Ibrahim a matsayin sabon shugaban NYSC.

Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na jami’an sojin Najeriya, Sagir Musa shine ya bada wannan sanarwa, inda ya bayyana cewa an dauka Ibrahim ne daga Jami’ar Soji dake Biu a jijar Borno.

Har ila yau, wasu nagani an sabawa doka saboda hukumar soji bata da hurumin nada sabon shugaban NYSC. Inda suka lura cewa shugaban kasa ne kadai yake da ikon yin hakan.

Wadanda ke wannan korafin sun kafa hujjojinsu ne akan dokokin hukumar NYSC inda suke cewa a wurare da daman a sassan dokar hukumar NYSC sam hakan bai dace kuma ya sabawa doka.

Sai ga shi kwatsam majalisar dattawa ta raba gardama a ranar Alhamis inda take cewa, babu wata tangarda dangane da nadin Shuaibu Ibrahim a matsayin sabon shugaban NYSC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel