Hudu ga watan Ramdana: Shin azumi dabi’ace ko ibada mai cike da takawa?

Hudu ga watan Ramdana: Shin azumi dabi’ace ko ibada mai cike da takawa?

-Watan Ramadan wata ne wanda yake da kyau musulmi ya nemi gafarar Allah a cikinsa

-Yayin bude baki lokaci shan ruwa an so masu hali su tuna da marayu da kuma marasa hali domin neman albarkar Allah cikin dukiyoyinsu

Ilahirn al’ummar musulmin duniya na gudanar da azumi a cikin watan Ramadana bisa ga koyarwar Alkur’ani mai girma.

Ya zo a hadisin annabi Muhammad (tsira da aminci Allah su tabbata a gareshi): “ Hali mai kyau dabi’a ce hali mara kyau kuwa laifi.” (Sahih Ibn Hibban da Sunan Ibn Majah). Wannan zancen daya fito daga bakin annabi Muhammad (SAW) shine ya kawo tambayoyi masu alaka da ibadar wannan wata mai alfarma domin samun karin takawa da kuma kusanci zuwa ga Allah.

Hudu ga watan Ramdana: Shin azumi dabi’ace ko ibada mai cike da takawa?

Hudu ga watan Ramdana: Shin azumi dabi’ace ko ibada mai cike da takawa?
Source: UGC

KU KARANTA:Shirun Buhari na damun mu, inji yan majalisar dokokin APC

Wadannan kyawawan dabi’un da ya kamata mu lura dasu manzon Allah ya sake jaddada mana su a cikin wani hadisi: “ Mutum bai zai gushe yana fadin gaskiya ba face sai an rubutashi a wurin Allah da cewa shi mai gaskiyane. Sannan kuma mutum ba zai gushe ba yanata yin kayar da goyon bayan karya face an rubutashi cikin makaryata.” (Sahihul Bukhari da Muslim).

Idan muka kasance muna tayi abu guda zai kasance dabi’a a garemu. Yau da gobe kuwa zai zama ma idan har ba muyi ba baza muji dadi ba.

A duk lokacin da mutum ke kokarin fadin gaskiya ko akan karan kansa ne, to hakika gaskiya ta zame masa jiki. Tabbas Allah zai daukaka wannan mutum zuwa mataki Siddik (wato mai gaskiya).

Ga ma’abota fadar gaskiya, gaskiya na kasancewa dabi’arsu. Kuma hakan bai cire fadar gaskiya daga cikin kyawawan ayyukan da addininmu ya koyar damu ba.

Annabi Muhammad, bai bambamce tsakanin dabi’a da kuma dorewa akan aikata alheri ba. Ga abinda yace “ Mafi soyuwa ga Allah daga cikin ayyukan alheri sune wadanda aka dauwama akansu komi kankantarsu.” (Sahihul Bukhari da Muslim).

Samun istikama akan aikin alkhairi na samuwane idan mutum ya rike sallah tare da tsantsar jin tsoron Allah. Wajibine mu tuna cewa Allah mai Rahama da jin kai ba shar’anta mana azumin Ramadan ba domin mu galabaita sai dai domin mu kara jin tsoronsa.

A karshe duk sanda zamuyi bude baki, mu tuna wadanda basu da abinci sai mu basu sadaka domin samun lada wurin Allah. Kada mutum ya rinka duba kanshi kawai ya manta da wasu yayin bude baki. Akwai marayu masu bukatar taimakonmu a wannan wata.

Allah Ya karbi ibadarmu cikin wannan watan mai albarka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel