Fashi da makami da sace-sacen mutane ba jarrabawa daga Allah bane – Shehu Sani ga babban limami

Fashi da makami da sace-sacen mutane ba jarrabawa daga Allah bane – Shehu Sani ga babban limami

- Ra’ayin Sheik Abdulwaheed Sulaiman na cewa annobar rashin tsaro da muggan ayyuka a Najeriya jarrabawa ne daga Allah ya hadu da suka

- Sanata Shehu Sani a shafinsa na Twitter ya mayar da martani ga limamin sannan yayi watsi da matsayarsa

- Sani ya bayyana cewa sace-sacen mutane da fashi da makami sakamako ne na gazawar gwamnatin baya da mai mulki

Sanata Shehu Sani ya mayar da martani ga babban limamin fadar Shugaban kasa, Sheik Abdulwaheed Sulaiman, wanda a ranar Laraba, 8 ga watan Mayu, ya bayyana cewa sace-sacen mutane da fashi da makami a kasar jarrabawa ne daga Allah.

A shafinsa na Twitter, Sanata Sani ya koka akan matsayar Sulaiman, inda ya kara da cewa halin da rashin tsaro ke ciki a Najeriya ya kansance sakamakon gazawar gwamnatin baya da na yanzu.

Sanatan ya ci gaba da bayyana cewa jawabin limamin na daidai da al’adan malaman fadar shugaban kasa wadanda, a cewarsa suna yiwa talakawa wa’azi da wuta sannan su yi wa masu mukami da karfi a kasa Magana da taushin murya.

KU KARANTA KUMA: Takarar neman shugabancin majalisa da nake ya samo asali ne daga abokan aikina – Lawan Ahmed

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Suleiman ya bayyana yawan lamarin miyagun ayyuka, kashe kashe da garkuwa da mutane a kasar a matsayin jarrabawa daga Allah.

Suleiman ya bayyana cewa muddin ana son a rabu da mumunan lamarin, yan Najeriya su nemi yafiyar Allah bisa zunubansu su kuma gudanar da addu’a ga Allah.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel