Yadda muka kama Mohammed Khalid a Najeriya - Kasar Amurka

Yadda muka kama Mohammed Khalid a Najeriya - Kasar Amurka

A ranar Alhamis ne gwamnatin kasar Amurka ta bayyana cewar hukumomin tsaro a Najeriya sun taimaka mata wajen kama wa tare da fitar da Muhammad Khalid Khan zuwa kasar Amurka.

Jakadan kasar Amurka ne ya bayyana hakan a Legas, ya ce kama Khan ya biyo bayan umarnin da sshen shari'a a kasar Amurka ya bayar a New York.

Gwamnatin Amurka na tuhumar Khan da safarar miyagun kwayoyi zuwa cikin kasar tare da shiga da makudan kudi ba bisa ka'ida ba.

Jakadan ya bayyana cewar Khan kwararre ne wajen safarar kwayoyi da kudi zuwa kasashen duniya a nahiyar Australia, Africa da Turai.

"Sashen shari'a na kasar Amurka tare da taimakon hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na Najeriya (NDLEA) ya samu nasarar kama wa tare da mayar da Muhammad Khalid Khan zuwa Amurka.

Yadda muka kama Mohammed Khalid a Najeriya - Kasar Amurka

Shugaban kasar Amurka; Donald Trump
Source: UGC

"An samu nasarar kama Khan ne bayan bangaren shari'a na tarayya a New York ya bayar da izinin kama shi domin mayar da shi kasar Amurka domin ya fuskanci hukunci. Sashen shari'ar ya dogara ne da taimakon jami'an tsaron Najeriya domin samun nasarar kama Khan," a cewar jawabin da jakadan Amurka ya fitar.

Ya kara da cewa an samu nasarar fita da Khan daga Najeriya zuwa kasar Amurka a ranr 28 ga watan Afrilu.

DUBA WANNAN: Majalisar dattijai ta tabbatar da hadimar Buhari a matsayin shugabar hukumar NDC

A cewar ofishin jakadancin Amurka, za a yanke wa Khan hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari a kan kowacce tuhuma da ake yi masa muddin kotu ta same shi da laifin da ake tuhumar sa da aikata wa.

Ofishin jakadancin ya ce zai cigaba da hada kai da hukumomin tsaron Najeriya da sauran kasashen duniya domin kama 'yan ta'adda tare da hukunta su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel