Buhari ya tabbatar da nadin sabon shugaban hukumar matasa masu yi wa kasa hidima NYSC

Buhari ya tabbatar da nadin sabon shugaban hukumar matasa masu yi wa kasa hidima NYSC

-"bada mukamin ya dace da dokar da NYSC ta tanada , kuma ba dokar da aka karya don an samu amincewar shugaban kasa kafin bada mukamin."

- Rundunar sojojin ta mika sunayen mutane ukku ga Buhari dangane da mukamin.

Rundunar sojojin Najeriya tace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da nadin Shu’aibu Ibrahim a matsayin shugaban hukumar matasa masu yi wa kasa hidima NYSC.

Bayanin sojojin na kunshe ne a cikin wani rahoton kwamitin majalisar dokoki wanda ya binciki bada mukamin da aka yi.

A cikin watan Mayu, rundunar sojojin ta sanar da nadin Ibrahim a matsayin sabon shugaban hukumar NYSC, abunda ya jawo cece-kuce daga bangarori da dama cewa fadar shugaban kasa ce ya kamata ta sanar da maye gurbin Suleiman Kazaure, wanda Ibrahim ya gada.

KU KARANTA: Yadda na tsallake talalabiyar tsigewa daga kujerar shugaban majalisa na tsawon shekaru 8 - David Mark

A shekara 2011, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada Thompson Okorie-Affia a matsayin shugaban hukumar, kuma daga baya a shekara 2013 ta nada Johnson Olawumi don maye gurbin shi. Buhari kuma ya nada Kazaure a shekarar 2016.

Sashe na 5 na dokar NYSC tace shugaban kasa ne kawai ke da damar bada irin wannan mukamin

Sagir Musa, mai magana da yawun rundunar sojoji yaki cewa komai kan al’amarin a lokacin da kafar watsa labarai ta TheCable ta tuntube shi.

Tun farko majalisar dokiki ta ba kwamitinta mai kula da sha’anin matasa da wasanni alhakin bincika yadda aka bada mukamin don gano ko an karya doka.

A wani zama ranar alhamis, Ogba Obinna, shugaban kwamitin ya karanto cewa GAT Ochigbano, mukaddashin sakataren sojoji yace rundunar sojojin ta mika sunayen mutane ukku ga Buhari dangane da mukamin.

Yace kwamitin ya gano cewa “bada mukamin ya dace da dokar da NYSC ta tanada , kuma ba dokar da aka karya don an samu amincewar shugaban kasa kafin bada mukamin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu. Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel